Skip to main content

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA
Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane

Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode.

AMSA
   Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,
   Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,
   Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,
   Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamullaili da azumi da istigfari, kuma kina iya lazimtar wannan addu'ar domin shi ANNABI MUSA yayi ya sami aikin yi da matar aure a ranar, ga addu'ar
رب إني لما أنزلت إلي من خير فقير

"Rabbi inni limaa anzalta ilaiya min khairin faqeer"

ALLAH yayafe mana kuma yabaki miji nagari,
ALLAHU A'ALAM.

Amsawa✍
Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN

Tambaya : Assalamu alaikum Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu : wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda daya ? don Allah mlm taimaka min da bayani. Amsa :  Wa alaikum assalamu To 'yar'uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za'a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma'a, za mu fahimci haka, a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara" Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban. Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : " Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal" ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a : sharhurmumti...