Skip to main content

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA

A
SHARI’AR MUSULUNCI



              NA
MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO.
FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe):



HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA:

Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai :

1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce:

“Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4).

A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:

  “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25).

2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :

 “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7).

An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa mene ne hakkin matar dayanmu a kansa, sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce :

“Ka ciyar da ita idan ka ci, ka yi mata tufafi idan ka yi tufafi, ko kuma idan ka samu, kada ka doki fuskarta, kada kuma ka munanata (wato ka yi mata ba’a) kada kuma ka kaurace mata sai a cikin daki”. Abu Dawud ne ya rawaito shi.

Kai! Musulunci ya bawa mace dama ta dauki abin da zai ishe ta daga dukiyar mijinta, idan yana da shi, kuma baya bata abin da zai ishe ta, An karbo daga Hindu bintu Utbah, ta ce :

“Ya Manzon Allah, Abu Sufyan mutum ne mai kwauro, baya bani abin da zai isheni, ni da yayana, sai dai abin da na dauka daga gare shi bai sani ba. Sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ki debi abin da zai ishe ki da 'ya'yanki a bisa adalci”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

3 – TUFATARWA DA WURIN ZAMA: Hakkin mace ne akan mijinta ya tufatar da ita gwargwadon samunsa, hadisin da ya gabata ya nuna haka. Haka nan hakkinta ne ya zaunar da ita a duk inda yake zaune, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana zaune da matan shi a gidansa, kamar yadda lamarin yake a zamanin sahabbai, su suke tanadar da wurin da zasu zauna da matansu. Haka nan Allah Madaukakin Sarki ya yi umarni ga mazaje su zauna da matansu wadanda suka saki (Sakin kome) a gidajensu inda suke zaune, Allah ya ce:

 “Ku zaunar da su a inda kuke zaune…”. Addalak: 6

4 – ADALCI A TSAKANINSU: Hakkin Mace akan mijinta ya yi mata adalci a tsakaninta da abokan zamanta. Allah Madaukakin Sarki ya umarci wanda ba zai iya adalci tsakanin matanshi ba da ya haqura da guda daya ko kuma kuyangi, Allah ya ce :

“Idan kuna jin tsoro baza ku yi adalci ba akan marayu mata (da aka bar muku ba, wadanda kuke so ku aura) to ku auri abin da ya yi dadi daga mata, bibiyu, da uku-uku da hurhudu. Idan kuna tsoron ba za ku yi adalci ba to ku (auri) daya, ko abin da damanku ta mallaka, wannan shi ya fi kusa da baza ku karkace ba”. (Nisa’i : 3).

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ya ce :

“Duk wanda yake da mata biyu, ya karkata zuwa ga dayarsu, to ranar alkiyama zai zo, gefensa a karkace”. Abu Dawud ne ya rawaito shi. Don haka wajibi ne namiji ya yi adalci tsakanin matanshi, sai dai an yi rangwame dangane da abin da yake zuciya, kamar so, da saduwa, saboda wannan dan adam bashi da iko a kai.

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

“Ba zaku iya daidaita (Son ku da saduwarku da sauran su) a tsakanin mata ba, koda kun yi kwadayin hakan, don haka kada ku karkata (ga daya) dukkan karkata, ku bar (dayar) kamar wadda aka rataye”. (Nisa’i : 129).

 Don haka idan miji ya ji yafi son daya akan daya, ko ya fi saduwa da daya akan daya, to wannan Allah ba zai kama shi da wannan ba, sai dai idan ya karkata dukkan karkata ga wannan da ya fi so, ya bar daya matar ta shi, kamar wadda aka rataye, ita ba mai miji ba, ba kuma wadda ba ta da miji ba. Allah ya kiyaye mu daga zalunci.

5 – KYAUTATA ZAMA DA MU'AMALA MAI KYAU: Hakkin mace ne, mijinta ya yi mata mu’amala mai kyau, ya yi kyakkyawan zamantakewa da ita, Allah Madaukakin Sarki ya ce :

“Ku zauna da su da kyakkyawan abin da aka sani na zama” (Annisa’i : 19).

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma yana cewa :

“Ina muku wasiyya da mata, saboda mace an halicceta ne daga kashin hakarkari, kuma mafi karkatar kashin hakarkari shi ne na saman shi, idan zaka mikar da shi to sai dai ka karya shi, idan kuwa ka kyale shi, haka zai zauna a karkace, ina muku wasici da mata”. Bukhari da Muslim.

A wani Hadisin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya yi:

“Mafificinku, wanda yake mafifici a wurin iyalansa. Ni ne mafificinku ga iyalaina”. Ibnu Majah.

Yana cikin kyakkyawan zama da mu’amala mai kyau, magidanci ya zama mai kyakkyawar magana, mai sakin fuska, mai zama da iyali yana debe musu kewa, mai musu kwalliya da ado, kamar yadda Ibnu Abbas yake yi, kuma yake cewa :
 “Ina yiwa mace kwalliya kamar yadda nake son ta yi min kwalliya”. Haka nan yin sallama yayin shiga gida, girmama yan uwanta, kula da ita idan bata da lafiya, yin haquri da ita, da afuwa da yafiya yayin da ta yi kuskure, kare ta daga duk abin da zai cutar da ita a addininta ko a duniyarta, da sauransu.

6 – ILMANTAR DA ITA: Hakkin mace ne akan mijinta ya ilmantar da ita, ya sanar da ita tsarkake Allah a ibada, da nisantar bautar waninsa, ya koya mata yadda ake bautawa Allah, kamar yadda Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koyar, domin Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

“Ya ku wadanda suka yi imani, ku kare kanku da iyalanku daga wata wuta, makamashinta mutane da duwatsu…” (Attahrim : 6).

Haka kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa Malik Bin Huwairis shi da abokansa yayin da suka zo wajensa, suka yi kwana ashirin, sannan suka yi niyyar komawa gida, sai ya ce da su:

 “Ku koma wajen iyalanku, ku koyar da su, ku umarce su, kuma ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yi”. Bukhari ne ya rawaito shi.

7 – BIYAN BUKATAR AURE: Hakkin mace ne akan mijinta ya biya mata buqatar aure, saboda yana daga cikin babban manufar aure a musulunci kare mace ko namiji daga afkawa cikin haramun. Allah Madaukakin Sarki ya yi mana gamonkatar.

RUFEWA:
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya bani dama da iko na rubuta dan abin da ya sauwaka gare ni, da fatan Allah ya sanya albarka a cikinsa.

Bayan haka, a cikin abin da ya gabata zamu ga adalcin addinin musulunci, ta inda ya baiwa kowa hakkinsa, kamar yadda ya dace da shi, haka kuma zamu ga akwai hakkokin da miji da mata suke tarayya a cikinsu, kamar hakkin kwanciyar aure da kyakkyawan zama da juna da sauransu, wadanda wasu malamai sukan ware su da bayani.

Haka nan da abin da ya gabata zamu gane buqatar sanar da mutane wadannan hakkoki, saboda da yawa daga cikin rikice-rikicen aure da suke tasowa daga jahiltar wadannan hakkoki ne, don haka idan aka samu wayar da kai, da karantar da mutane wadannan hakkoki, ko shakka babu za a samu raguwar rigingimu da rikice-rikicen aure. Allah ya sa mu dace.

 A karshe nake cewa, wannan shi ne abin da Allah ya hore min in rubuta a kan wannan matashiya mai matukar mahimmanci, kuma na yi kokarin ambaton manya-manyan hakkoki ne na kowanne bangare, miji da mata, amma ba ina nufin iyakar su kenan ba, a’a, na yi ne a takaice, don haka kofar kari a bude take, ana kuma iya komawa manya-manyan littattafan malamai don ganin wadannan hakkoki.

 Allah Madaukakin Sarki ya sa mu dace, ya kuma gafarta mana kurakuranmu. (Ameen).

Zauren FIQHUS SUNNAH 08142082937

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...