Skip to main content

Posts

Recent posts

INA SON KARIN BAYANI AKAN SITTU SHAWWAL !

Tambaya Assalamu alaikum, Malam don Allah ayi min bayani akan shittu shawwal !! Amsa Wa alaikum assalam  Sittu Shawwal azumi ne da ake yinsa guda shida a watan Shawwal, wato watan da muke ciki yanzu haka. Azumin yana da falala ga wanda ya samu iko, saboda ba wajibi ba ne, Annabi (SAW) yana cewa: "Duk wanda ya yi azumin watan Ramdhana kuma ya biyo shi da azumi shida a Shawwal zai samu ladan azumin shekara guda" kamar yadda Muslim ya rawaito daga Hadisin Abu-ayyub. Ya halatta a rarraba azumin sittu Shawwal, bai zama dole ayi shi a jere ba. Mace mai haila za ta fara rama azumin da ake binta kafin ta yi Sittu Shawwal, hakan nan Mara lafiya ko mai SHAYARWA, kamar yadda hadisin da ya gabata yake nunawa !! Allah ne mafi Sani Amsawa  ✍️ DR. JAMILU YUSUF ZAREWA daga  ZAUREN FIQHUS SUNNAH

SUNNONI DA LADUBBAN RANAR IDI

SUNNONI DA LADUBBAN RANAR IDI 1️⃣ YIN WANKA KAFIN FITA SALLAH Ya inganta a cikin Muwaɗɗa na Imamu Malik, Rahimahullah, 428, cewa: Abdullahi Ɗan Umar, Radhiyallahu anhu, ya kasance yana yin wanka kafin ya fita sallar idi.  2️⃣ CIN ABINCI KAFIN FITA IDI IDAN KARAMAR SALLAH CE DA KUMA CIN ABINCI BAYAN IDI IDAN IDIN LAYYA NE: Hadisi ya inganta daga Anas Ɗan Malik cewa: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya kasance ba ya fita sallar idi na karamar Sallah har sai ya ci dabino kuma ya kan ci mara ne ( wato 1 ko 3 ko 5 ko 7...). Bukhari ya riwaito 953. Duk wanda bai samu dabino ba sai ya ci daga abun da ya halasta.  Amma dangane da Idin layya an so wanda zai yi layya kar ya ci komai har sai bayan sallar idi sai ya ce daga dabbar layyan shi.  Wanda kuma bai da dabban da zai yi layya babu laifi idan ya ci abinci kafin sallar idi.  3️⃣ KABBARBARI A RANAR IDI  Ibn Abi Shaibah ya riwaito da isnadi ingantacce daga Al-Zuhriy cewa: Mutane sun kasance suna yin kabbara ...

WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR IDI

Tambaya Assalamu Alaikum,  Malam ina so sanin hukunce-hukuncen idi  Amsa Wa'alaikumus salam. Idi yana da hukunce-hukunce da yawa ga wasu saga ciki: 1. Azumtar ranar idi – ya haramta a azumci ranakun idi guda biyu, saboda hadisin Abu-sa'id Al-kudry, -Allah ya yarda da shi - cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana azumtar ranaku biyu – wato ranar karamar sallah da ranar babbar sallah" Muslim ya rawaito 2. Siffar sallar idi- An karbo daga Abu-sa'id -Allah ya yarda da shi – cewa : "Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana fita ranar idin karamar sallah da babbar sallah zuwa filin idi, idan ya fita yana farawa da sallah" Bukari ne ya rawaito Ana yin ta ne raka'o'i biyu, za'a yi kabbara bakwai a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma sai ayi kabbara shida. Abu-dawud  Idan mamu ya riski limaminsa a tsakiyar kabbarori, to zai yi kabbarar harama ne ya bi shi, ba zai rama abin da...

WASU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN DA SUKA SHAFI RANAR ID

ZA'A IYA FITARWA DA KIRISTA ZAKKAR FIDDA KAI ??

Tambaya Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ina yiwa mlm fatan alkhairi, Allah ya kara budi. Wasune suke neman fatawan akan wnn mas'alar "musulmine yake auren Christian, to wai idan zai fidda zakkar fidda kai itama zai fitar mata?" Amsa Wa alaikum assalam Hadisi ya tabbata daga Ibnu Umar cewa: "Annabi (SAW) ya farlanta zakkar fiddakai akan kowanne musulmi Da ne ko bawa" kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito. Hadisin da ya gabata yana nuna musulmi ake fitarwa zakkar fiddakai, amma kafiri ba'a fitar masa, kuma ba'a shi in an fitar. Allah ne mafi sani Amsawa ✍🏻 DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

ZAN YI AZUMI TALATIN DA DAYA (31)

Tambaya Assalamu Alaikum malam Tambayata ita ce malam idan mutum ya fara Azimi a qasar Nigeria, sai yaje wata qasa misali qasar saudiya sai Azuminsu ya kai talatin, kai kuma idan ka ida wannan Azumi tare da su to Azuminka zai zama talatin da daya, menene mafita ? Amsa Waa alaikumus Salam,  To dan'uwa za ka cigaba da azumi ne tare da su, har sai sun sauke, saboda fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Ana shan ruwa ne ranar da mutane suka sha ruwa" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 697 kuma Albani ya inganta shi a silsilatussahihah 224 . A bisa wannan hadisin wanda ya je Saudiyya a wannan shekarar ta 1435, ba zai sauke azumi ba har sai sun sauke, ko da kuwa zai yi talatin da daya ne, kamar yadda wanda ya dauko daga Saudiyya ya taho Nigeria zai sauke azuminsa lokacin da suka sauke, ko da kuwa zai zama ashirin da takwas ne, saidai zai rama daya bayan sallah. Allah ne mafi sani  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa