SUNNONI DA LADUBBAN RANAR IDI
1️⃣ YIN WANKA KAFIN FITA SALLAH
Ya inganta a cikin Muwaɗɗa na Imamu Malik, Rahimahullah, 428, cewa: Abdullahi Ɗan Umar, Radhiyallahu anhu, ya kasance yana yin wanka kafin ya fita sallar idi.
2️⃣ CIN ABINCI KAFIN FITA IDI IDAN KARAMAR SALLAH CE DA KUMA CIN ABINCI BAYAN IDI IDAN IDIN LAYYA NE:
Hadisi ya inganta daga Anas Ɗan Malik cewa: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya kasance ba ya fita sallar idi na karamar Sallah har sai ya ci dabino kuma ya kan ci mara ne ( wato 1 ko 3 ko 5 ko 7...). Bukhari ya riwaito 953.
Duk wanda bai samu dabino ba sai ya ci daga abun da ya halasta.
Amma dangane da Idin layya an so wanda zai yi layya kar ya ci komai har sai bayan sallar idi sai ya ce daga dabbar layyan shi.
Wanda kuma bai da dabban da zai yi layya babu laifi idan ya ci abinci kafin sallar idi.
3️⃣ KABBARBARI A RANAR IDI
Ibn Abi Shaibah ya riwaito da isnadi ingantacce daga Al-Zuhriy cewa: Mutane sun kasance suna yin kabbara a ranar idi daga lokacin da suka fito daga gidajensu har sai sun isa filin sallar idi sannan suna ci gaba da kabbarbari har sai liman ya fito... A duba Irwa'u al-Galil 2/121.
Sai dai lokacin kabbarbarin Idin karamar Sallah yana farawa ne lokacin da idi ya fara (ranar da aka ga wata) har sai liman ya fito sallar idi.
Amma kabbarbarin sallar idin layya yana farawa ne daga daya ga watan dhul-Hijjah zuwa karshen ranakun ayyamut tashreeq.
YAYA AKE KABBARBARIN?
Ya zo a Musannaf na Ibn Abi Shaibah da sanadi ingantacce daga Abdullahi Ɗan Mas'ud, Radhiyallahu anhu: ya kasance yana kabbara a cikin ayyamut tashreeq: ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LAA ILAAHA ILLAAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WA LILLAAHIL HAMD. A wata ruwayar ya ce za a yi kabbara sau 3.
A wata har wayau daga Abdullahi Bn Mas'ud: ALLAHU AKBAR KABEERAN, ALLAHU AKBAR KABEERAN, ALLAHU AKBAR WA AJAL, ALLAHU AKBAR WA LILLAAHIL HAMD. A duba littafin Irwa'u al-Galil 3/126.
4️⃣ YI MA JUNA MURNA (BARKA)
Daga Jubair Bn Nufair, ya ce: Sahabban Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, sun kasance idan suka haɗu a ranar idi sashensu kan ce ma sashe: Allah ya karɓa daga gare mu da ku (TAQABBALALLAHU MINNAA WA MINKUM). Fathu al-Baariy 2/446.
5️⃣ YIN KWALLIYA DOMIN IDI
Jabir, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, yana da wata alkyabba ta musamman da yake sanyawa ranar Juma'a da ranar idi.
Al-Baihaqiy, ya riwaito da isnadi ingantacce cewa Abdullahi Ɗan Umar, Radhiyallahu anhu, ya kasance yana sanya mafi kyawun kayan shi a ranar idi.
Dangane da mata kuma haramun ne su sanya kaya mai kwalliya su fita da shi zuwa masallaci kamar yadda haramun ne su shafa turare.
6️⃣ CANJA HANYA YAYIN DAWOWA DAGA IDI
Hadisi ya inganta daga Jabir Ɗan Abdullahi, Radhiyallahu anhumaa, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya kasance idan ranar idi ta zo yana canja hanya. (wato idan ya je ta wata hanya idan zai dawo sai ya canja hanya). Bukhari ya riwaito 986.
Da fatan zamu nisanci duk wani aiki da zai bata mana ladan Ibadan da muka gabatar.
Ni ma Ɗan uwanku Umar Shehu Zaria ina cewa daku: TAQABBALALLAHU MINNAA WA MINKUM.
✍️ Ɗan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
Comments
Post a Comment