Tambaya
Assalamu alaikum,
Malam don Allah ayi min bayani akan shittu shawwal !!
Amsa
Wa alaikum assalam
Sittu Shawwal azumi ne da ake yinsa guda shida a watan Shawwal, wato watan da muke ciki yanzu haka.
Azumin yana da falala ga wanda ya samu iko, saboda ba wajibi ba ne, Annabi (SAW) yana cewa: "Duk wanda ya yi azumin watan Ramdhana kuma ya biyo shi da azumi shida a Shawwal zai samu ladan azumin shekara guda" kamar yadda Muslim ya rawaito daga Hadisin Abu-ayyub.
Ya halatta a rarraba azumin sittu Shawwal, bai zama dole ayi shi a jere ba.
Mace mai haila za ta fara rama azumin da ake binta kafin ta yi Sittu Shawwal, hakan nan Mara lafiya ko mai SHAYARWA, kamar yadda hadisin da ya gabata yake nunawa !!
Allah ne mafi Sani
Amsawa ✍️
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment