Huduba Daga Masallaci Mai Alfarma
Yau Jum'ah 18 ga Dhul Hajj 1436H (2/10/2015)
A yau Sheikh Su'ud As-Shuraim - daya daga cikin limaman masallaci mai alfarma - ne ya jagoranci sallah a masallacin Makka mai daraja bayan ya yi huduba a kan cikar addini da hadarin yin bidi'a a cikin sa.
Sheikh ya soma hudubarsa da gode ma Allah a kan ni'imar kammala aikin Hajji wanda a tsakiyar aiwatar da shi ne Allah ya shelanta ma manzonsa cewa ya cika ma wannan al'umma addininta.
A cikin wannan Hajji Manzon Allah (S) ya yi hasashen kusantowar ajalinsa.
Limamin ya fashe da kuka a lokacin da yake bayanin kamalar addinin musulunci da kasancewar manzon Allah (S) bai bar wani abu da ake bukatar bayanin sa a addini ba face ya bayyana shi kafin zuwan ajalinsa. Amma kuma musulmi da yawa ba su fahimci haka ba. Sai aka hada gaskiya da karya, aka farar da sababbin abubuwa da sunan wai musulunci dole ne ya canza riga don ya dace da zamani. Akwai mamaki ace kafiri arne wanda ya rayu a cikin musulmi ya fi musulmin fahimtar wannan aya. Domin wani bayahude ya ce ma Sayyidi Umar akwai aya a cikin littafinku in da muna da irin ta da mun mayar da ranar saukar ta ranar buki ta shekara shekara. Yana nuni zuwa ga sanin muhimmancin kammala addini, abinda musulmi da yawa ba su fahimce shi ba.
A yau wasu wawaye sun mayar da addini bakauye, suna dauka cewa, ba zai dace da zamani ba wai sai an yi masa gyaran fuska.
Ku sani ya ku musulmi! Wallahi babu sadda zamu iya shiga gaban manzon Allah ko mu fi shi iya ganewa da fahimtar addini.
Allah ya cika addininmu, bai bar wani alheri ba sai da ya nuna mana shi. Kuma duk wata lalura da zata faru ko wata bukata da za ta auku ga yan Adam akwai bayanin ta a cikin musulunci ba sai mun yi aro daga wajen sa ba.
Musulunci ya karantar da yan uwantaka da kyautatawa da fahimtar juna, duk a karkashin Kalimatus Shahada.
Allah ya yi kira ga mu kauce ma shaidan wanda babban makiyi ne a gare mu.
A cikin huduba ta biyu, liman ya jaddada gode ma Allah sannan ya ce, duk matsalolin da al'umma take fama da su ba sababbi ba ne kuma ba wani abu ya jawo su ba sai kauce ma hanya da musulmi suke yi. Abinda yake faruwa a Syria zalunci ne da ake yi a kan talakawa.
Sannan liman ya yi nuni ga hassada da kyashin da kasar Iran take yi ma kasa mai tsarki da kulle kullen da take yi mata dare da rana yana mai nuni ga abinda suka haifar na tashin hankula da kashe jama'a sannan suka ruga majalisar dunkin duniya suna cewa Saudi ba ta iya ba. A ba su dama su shigo kasa mai tsarki su yi hidimar alhazai. Ya ce, a wannan kasa muna da doka, muna da tsari, a kan Sharia muke tafiya, kuma ba zamu taba buda kofa a wargaza mana akida ko a taba mana zaman lafiya ba. Kuma maganar Allah ba ta tashi, lalle ne zai taimaki muminai.
Liman ya rufe hudubarsa da addu'oi masu kyau masu dadi, masu albarka.
Ya sake fashewa da kuka a lokacin da yake yi ma alhazzai addu'a musamman wadanda suka hadu da matsaloli da jarabawa a cikin aikin hajji.
Ya Allah ka karbi adduoinsa, ka wanzar da aminci a cikin musulmi, ka kare mu daga makircin makiya.
Fassara daga Dr Mansur Sokoto.

https://fiqhussunnah.blogspot.com/2015/11/huduba-daga-masallaci-mai-alfarma-yau.html?showComment=1538185184096#c5120439243557533275
ReplyDeleteThis comment has been removed by a blog administrator.
ReplyDelete