MATA ZA SU IYA YIN SALLAR JANA'IZA ?
Tambaya:
Slm, malam ya halatta mata subi sallar jana'iza? saboda na ga wani malami lokacin da aka kashe masa yaya har mata ya tara aka yi musu sallar jana'ixa Ngd malam
Amsa :
To dan'uwa ya halatta mata su yi sallar jana'iza, saboda dalilan da suka zo akan sallar jana'iza ba su banbance tsakani mace da namiji ba.
Duk nassin da ya zo daga Al'qur'ani ko sunna, to yana hade maza da mata wajan hukunci, in ba'a samu wani dalili ko alama wacce ta fitar da su daga ciki ba .
Sannan mata sahabbai sun yiwa Annabi s.a.w. sallah bayan ya mutu, babu kuma wanda ya yi inkarin hakan, sai wannan ya nuna shi ne shari'a.
Allah ne mafi sani .
Jamilu Zarewa
11\5\2015
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment