Skip to main content

MUNA ZUBAR DA CIKI NI DA MIJINA IDAN LIKITA YA GAYA MANA YARON DA ZAMU HAIFA SKILA NE

MUNA ZUBAR DA CIKI NI DA MIJINA IDAN LIKITA YA GAYA MANA YARON DA ZAMU HAIFA SKILA NE:

TAMBAYA:
Slm mallam ni AS ce mijinama ma desame genotype muke dashi yarana biyu babban AA karamar AS duk sanda na sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn dake chikin likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a chire amma bai kaiwa 4months muke chirewa mallam meye hukunchin yin hakan


AMSA:
Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu,

To 'yar'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Scler ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.    

 Allah ne mafi sani.  

Dr Jamilu Zarewa  18/10/2015

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...