MUT'A KO DAI ZINA!
NaMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 1:
BABI NA FARKO
MA'ANAR AUREN MUT'A
(1) SUNNA: Ma'anar sa a shari'a shine jin dadi, amma ma'anar sa a ilmin fiqhu shine mutum ya auri mace da wani abu na dukiya ayyananne, tsawon lokaci ayyananne, auren na karewa da karewarsa ba tare da saki ko wajibcin ciyarwa ko wurin kwana ba, kuma babu gadon juna a tsakaninsu da dayansu zai mutu kafin karewar auren.
(2) SHI'A: Shi kuwa babban malamin Shi'a "Abdul Husain Sharafuddin Almusawi" cewa yayi: "shine mace ta aurar maka da kanta da wani sadaki ambatacce, da kulla auren da ya taro sharuddan ingancin aure na shari'a, wanda babu abinda Shari'a ta hana kamar yadda ka ji, sai ta ce maka bayan an sami musayar yarjejeniya da amincewa a tsakanin juna: "Na aurar maka ko na mut'antar maka kaina da sadaki gwargwadon sa kaza, kwana daya ko kwana biyu ko wata biyu ko shekara daya ko shekara biyu ga misali, ko ta ambaci tsawon lokaci ayyananne a bisa ka'idah, sai kai kuma kace mata da gaggawa: "Na amsa".
Mu hadu a fitowa ta biyu, in sha Allahu Ta'ala.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment