MUT'A KO DAI ZINA!
NAMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 2:
MA'ANAR MUT'A A SHI'A.
Wakikci yana halatta a cikin wannan kulli daga dukkan ma'auratan biyu, kamar waninsa na kulle-kulle. Kuma da cikarsa be take zama mata a gare ka, kai kuma ka kake zama miji a gare ta, har zuwa karshen ajalin da aka ambata a cikin kulli (auren). Kuma yana karewa zata nisance ka ba tare da saki ba kamar jinga. Kuma mijin ya samu ya rabu da ita gabanin karewar ajalin da kyatar sauran kwanakin da suka rage ba tare da saki ba. Kuma yana wajaba tayi idda bayan ya take ta bayan kyautar lokacin ko karewarsa da tsarki biyu idan ta kasance daga cikin mata masu haila. Idan kuwa ba ta kasance daga cikin mata masu haila ba said ta yi idda ta kwana arba'in da biyar kamar baiwa".
ABUBUWAN DA MAI KARATU ZAI FAHIMTA:-
Lallai a cikin wannan ma'ana ta auren mut'a da shi wannan malamin shi'a ya ba mu, mai karatu zai fahimci abubuwa kamar haka:-
(a) Auren babu waliyyi, daga ita said shi aukayi,
(b) Itace ta aurar da kanta
(c) Abdul Husain bai ambaci daya daga cikin sharuddan aure ba kamar haka:- waliyyi, sadaki, shedu, ciyarwa, wurin kwana, saki, gado, da dai sauransu, sai dai ya ambaci dukiyar da zai bata (kamar dai yadda ake ba karuwa kudin jinga).
(d) Samuwar sharadi a cikin sa, na zuwa wani lokaci ayyananne wanda auren na karewa da karewar sa saboda haka shi wannan aure bashi da wani sharadi ingancin aure na sharia.
MAKIRCIN SHI'A A CIKIN WANNAN MA'ANAR
Muhadu a fitowa ta uku insha Allahu
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment