MUT'A KO DAI ZINA!
NAMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 3:
MAKIRCIN SHI'A A CIKIN WANNAN MA'ANAR
Karyar Abdul Husain, inda yake cewa: wanda babu abin da shari'a ta hana Alhali babu sharuddan aure a cikin sa.
FADAKARWA
Wannan ma'ana ta sabawa abinda na karanta a cikin Alkafi, daga "Abbana Dan Tagliba" yace: na cewa Abu Abdullahi (AS): Yaya zance mata idan na kadaita da ita? Sai yace: za ka ce ne: " Na aure ki auren mut'a a bisa littafin Allah da sunnar AnnabinSa (SAW) ba za ki yi gado ba kuma ba za a gaje ki ba tsawon kwana kaza-da-kaza. Idan kuma ka so, shekara kaza-da-kaza, da kaza-da-kaza na dirham. Sai ka ambaci abinda duk kuka yi yardatayya a kansa na lada, kadan ne ko mai yawa. Idan tace "na'am" to hakika ta yarda, saboda haka ta zamo matarka kai kuma ka zamo mijinta kuma mafi cancantar mutane da ita.
MUT'A A WURIN 'YAN SHI'A
Lallai mut'a tana da mahimmanci kwarai a wurin 'yan shi'a saboda haka suka kirkiro mata munanan Hadisai na karya, suna jinginasu zuwa ga Imaman Ahlul Baiti (AS), alhalin Imaman Ahlul Baiti sun barranta daga gare su irin barrantar kekeci daga jinin dan Annabi Ya'kub (AS). Saboda kada in tsawaita zan takaita da Hadisi daya kawai. Suna cewa wai Manzon Allah (SAW) yace: Duk wanda yayi mut'a sau daya darajarsa ta kasance kamar darajar Alhusain (AS) Imam na uku a wurin 'yan Shi'a, kuma duk wanda yayi mut'a sau biyu darajarsa ta kasance kamar darajar Alhasan (AS), Imam na biyu a wurinsu, kuma duk wanda yayi mut'a sau uku darajarsa ta kasance kamar darajar Aliyu Dan Abi Talib (RA) Imam na farko a wurinsu, kuma duk wanda yayi mut'a sau hudu darajarsa kamar darajata".
Nake cewa: ya kai mai karatu kaji duk wanda yayi mut'a sau hudu ya riski Annabi a daraja. Shin wanda yayi mut'a sau biyar fa?
Allah ka tsare mu da fadawa halaka.
BABI NA BIYU
Muhadu a fitowa ta hudu Insha Allahu Ta'ala.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment