MUT'A KO DAI ZINA!
NaMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 4:
BABI NA BIYU
AUREN MUT'A KAFIN YA ZAMO HARAM
Ya kai mai karatu! Allah ya shiryar da mu, shi auren mut'a an haramta shi ne sannu-sannu kamar yadda aka haramta shan giya sannu-sannu. Sannan kuma koda aka halatta yin sa an halattashi ne a halin tafiya, ba a halin zaman gida ba, a lokacin da sahabbai suna wata duniya domin jihadi, sha'awarsu ta yi tsanani, hakurinsu yayi karanci domin sun bar matansu a gida, kuma anaji masu tsoron fitina, kuma gasu suna sababbin musulunta, sai ya kasance daga cikin hikima a cire su daga alfasha sannu-sannu, sai ya zamo yana da hukunci irin na cin mushe ga wanda ya shiga cikin tsanani a wancan lokacin kafin a haramta yinsa.
Domin mai karatu ya san auren mut'a halal ne a farkon al'amari ga wasu Hadisai da suka nuna halaccin yin sa kafin ya zamo haram kuma wadannan Hadisai sune Malaman shi'a suke kafa hujjan halaccin mut'a da su daga littafan Ahlus-sunnah sai su kau da kai daga Hadisan da suke nuni akan haramcin yin sa, ko su karyata su, ko kuma su juyar da hakikanin ma'anar su, domin kawai sun sabawa ra'ayinsu na mut'a.
Ga Hadisan kamar haka:
(1) Daga Abdullahi Dan Mas'ud (R.A) yace: "mun kasance muna yaki tare da Manzon Allah (S.A.W) sai ya saukaka mana mu auri mace da tufafi zuwa wani lokaci".
A wani hadisin na Jabir shima ya ruwaito halaccin auren mut'a.
(2) Daga Jabir Dan Abdullahi da Salamata Dan Ak'wa'i (R.A) sun ce: Me yiwa Manzon Allah (S.A.W) yekuwa ya fito a garemu sai yace "Lallai Manzon Allah (S.A.W) yayi muku izni kuyi mut'a.
(3) Haka kuma a wata ruwayarta Ada'u yace : Jabir Dan Abdullahi yagabato domin Umra, sai muka zo masa a masaukinsa, sai muka tambaye shi game da wasu abubuwa, sannan sai suka ambaci mut'a, sai yace: "E mun yi mut'a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da Abubakar da Umar Dan Khattaab".
Shi kuwa wannan hadisin Jabir yana sake jaddada halaccin mut'a kafin haramtuwarta.
Mu hadu a fitowa ta biyar, Insha Allahu Ta'ala.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment