MUT'A KO DAI ZINA!
NaMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 5:
BABI NA BIYU
AUREN MUT'A KAFIN YA ZAMO HARAM
(4) An karbo daga Jabir Dan Abdullahi (R.A) yace: Mun kasance muna mut'a da damkar tafi na Dabino da Gari na wasu kwanaki a zamanin Manzon Allah (S.A.W) har Umar Dan Khattaab ya yi hani daga gare shi.
Wannan Hadisi na hudu wato hadisin Jabir yana daga cikin hadisan da 'yan shi'a suke jefa shubuhar su ga jahilai, saboda cewar da Jabir Dan Abdullahi yayi: (Mun kasance muna mut'a a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da Abubakar da Umar Dan Khattaab......) Imamun Nawawi ya warware shubuhar, yana cewa:
"Amma dalilin su daga Hadisin Jabir Dan Abdullahi (R.A) da yace: Munyi mut'a a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da Abubakar da Umar Dan Khattaab..., za'a dauki wannan ne akan cewa wadanda suka yi mut'a a zamanin Abubakar da wani yanki na halifancin Umar Dan Khattaab, labarin haramcin yin haka bai je gare su ba, daga cikinsu akwai shi kansa Jabir (R.A).
Wadannan sune kadan daga Hadisan da suka nuna halaccin auren mut'a kafin haramtuwar sa, saboda haka ne Malaman sunnah suka yi ijma'i akan halaccin auren mut'a a farkon musulunci na wasu kwanaki 'yan kadan kafin Manzon Allah (S.A.W) ya haramta shi haramci na har abada, kuma Wadannan hadisai babu shakka an shafe hukuncinsu da hadisan da suka haramta auren mut'a, kamar yadda Insha Allahu mai karatu zai gansu nan gaba kadan.
ABUBUWAN DA MAI KARATU ZAI FAHIMTA DAGA WADANNAN HADISAI:-
1- ba a halatta musu ba sai a halin tafiya.
2- Sun bar matan su a gida
3- Sha'awar su tayi tsanani.
4- Ana ji musu tsoron fadawa cikin fitina.
5- Halaccin na wani lokaci ne da bai wuce kwana uku ba.
6- Wadanda suka yi mut'a a zamanin Abubakar da wani yanki na halifancin Umar Dan Khattaab hanin bai kai garesu ba, daga cikin su akwai shi kansa Jabir Dan Abdullahi (R.A)
7- Tsanani ya sa aka halatta musu, saboda haka yake da hukuncin cin mushe ga wanda ya shiga tsanani a wancan lokacin.
MAKIRCIN SHI'A A CIKIN WADANNAN HADISAI
Rashin yiwa mabiya irin wannan bayanai domin kada su fahimci gaskiya.
Mu hadu a fitowa ta shida, Insha Allahu Ta'ala.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment