MUT'A KO DAI ZINA!
NaMuhammad Umar Ibrahim Gumau
FITOWA TA 6:
BABI NA UKU
LALURA CE TASA AKA HALATTA MUSU MUT'A
Duk mai bibiyan Hadisan da suka halatta mut'a a farkon al'amari, zai ga wannan halaccin bai kasance a halin zaman gida ba, kawai an halatta musu ne a cikin yaki mai nisa, da halin tafiya mai tsawo a lokaci da sha'awar su tayi tsanani, hakurinsu yayi karanci, kuma ana ji musu tsoron fadawa fitina, kuma ga su suna sababbin musulunta sai ya kasance daga cikin hikima a cire su daga alfasha sannu-sannu, kamar yadda aka haramta musu giya sannu-sannu.
Imamun Nawawi yana cewa:
Jama'a da dama sun ruwaito Hadisan mut'a, amma babu wani Hadisi da ya nuna cewa an halatta musu mut'a a halin zaman gida, kawai halaccin ya kasance ne a halin tafiyar su domin yakoki, a lokacin suna cikin larurar su na rashin kasancewarsu a kusa, tare da kasancewar garuruwansu sun kasance Mas'ud zafi, kuma hakurinsu ga barin mata ya yi karanci.
Kuma hakika an ambata acikin Hadisin Dan Umar Dan Khattaab cewa mut'a ta kasance abar saukakawa ce a farkon Musulunci ga wanda ya bukatu gare ta kamar dai cin mushe da abinda yayi kama da shi.
Mu hadu a fitowa ta bakwai, Insha Allahu Ta'ala.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH, sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.
Comments
Post a Comment