SHIN YA HALASTA IN YANKE DAGA GARE TA, SABODA TANA CUTAR DA NI?
Tambaya:
assalamu alaikum
mlm inada tambayane akan yake xumunci
mlm inda kawane nikuma ina karantar da mata ita kuma kawan tawa batada aiki sai batane a wajen dalibaina kuma mlm shakuwa da ita yakesa takemin haka shin zan iya kaurace mata kamar yadda mai AHLARI yafada
don so dayawa nakan kaurace mata saina samu sauki saikuma naga kamar nayanke zumunci saina sake koma mata yanxu abun yafaru kusan so 3 mlm ataimaka abani mafita tana cutar dani tana zubarmin da mutunci.
Amsa:
To farko dai ki yi mata wasiyya da tsoron Allah, sannan ki bayyana mata munin hakan, in har ta ki, za ki iya rage maamala da ita, saboda hakan zai iya rage kaifin matsalar da ke tsakaninku, rage mu'amala da ita ba zai zama yanke zumunci ba tun da ba 'yar'uwarki ba ce ta jini.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
12/10/2015.
Comments
Post a Comment