Skip to main content

TATAUNAWA TSAKANIN WANI MALAMIN SHI'A DA MABIYANSA  AKAN AUREN MUTU'A

TATAUNAWA TSAKANIN WANI MALAMIN SHI'A DA MABIYANSA  AKAN AUREN MUTU'A


Malamin shia:Assalamu alaikum

Dalibai:wa'alaikumu salam

Malamin shia: A yau karatun mu zai kasance ne akan Auren Mutu'a

Dalibai:Allah ya ja zamanin mallam

Malamin shia: Falalar Mutu’a

Akwai daruruwan ruwayoyi a cikin littafan malaman mu da suke izna da su wadanda suke nuna mana falalar auren mutu'a . Ya zo a cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih, daya daga cikin littafan mu  guda hudu mafiya inganci,cewa Ja’afar Sadik, wato Imamin mu na shida, cewa ya ce: “Lallai Mutu’a addinina ce kuma addinin iyayena. Wanda ya yi aiki da ita ya yi aiki da addininmu kuma wanda ya yi inkarin ta ya yi inkarin addininmu, kuma ya yi riko da wanin addininmu.”

Dalibai:Na'am

Malamin shia: Ya zo a wannan littafi har yau,cewa  Annabi (SAW)ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau daya zai
amince fushin Allah, wanda ya yi Mutu’a sau biyu za’a tashe shi tare da zababbun bayi, wanda ya yi Mutu’a sau uku zai hada kafada da ni a aljanna.”

A wata ruwayar mai kama
da wannan, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau daya za ta zama (gare shi) kamar darajar Hussaini (A.S); wanda ya yi Mutu’a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan (A.S) ce; wanda ya yi Mutu’a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali (A.S); kuma wanda ya yi Mutu’a sau hudu darajarsa kamar
darajata ce.

Dalibai: Allahu Akbar!!!!

Malamin shia: wai ko kun san ladan dake cikin Auren Mutu'a kuwa?

Dalibai: a'a Malam

Malamin shia: Alsaduq ya  Ya ce: an tambayi Abu Abdullahi, watau Imamin  na shida: Shin mai yin Mutu’a yana da lada? Sai ya ce, “In yana nufin yardar Allah da ita (Mutu’ar) ba zai yi magana da ita ba (matar) kalma guda face Allah ya rubuta masa lada da ita (kalmar), kuma idan ya kusance ta sai Allah ya gafarta masa zunubi, kuma idan ya yi wanka Allah zai gafarta masa da gwargwadon ruwan da ya shude a kan gashinsa.”

Dalibai: Ama mallam shine Ahlu sunnah suke inkarin irin wanan garabasa?

Malamin shia:ku daina kulla su

Dalibai:ai mu dama bama kulla su sai dai karatun su da suke yi a gidan rediyo shike tada mana da hankali.

Malamin shia: Hmmm ku kyale su muma za mu sayi fili mu rika mayar masu da martani.

Dalibai:Allah ja zamanin Mallam.

Malamin shia: mu koma karatu.   Gargadi ga Wanda Ya Qi Yin Mutu’a Bayan bayanin falala da garabasar Mutu’a, idan da akwai
wani mai taurin kai wanda ya ki dibar wannan garabasa, to To ga  gargadi da tsoratar wa ga wanda yaki diban wanan lagwada da garabasa .   Malamin mu  mai suna Alfailul Kashani, ruwaito daga Annabi (SAW) cewa ya ce:

“Wanda ya fita daga duniya bai yi Mutu’a ba, zai zo ranar
Alkiyama yana yankakke (watau nakisin halitta).”

Daya daga cikin dalibai: mallam a wani karatu na wahabiyawa da na ji sun ce wai a harshen Shari’a, irin wannan gargadi da ka ambato na wanda yaki yin mutu'a ana yin sa ne ga
wanda ya aikata kaba’ira, watau babban zunubi, kamar shaidar zur, ko gudu daga fagen fama, ko saba wa iyaye da sauransu.

Malamin shia: karya suke yi

Daya daga cikin Dalibai:mallam nima na ji wani karatu nasu cewa wai Wannan shi yasa ya sa Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da dan
Shi’a ne kuma Allah ya shirye shi ya tuba, yake cewa manyan malaman mu na wannan zamani, kamar su Sayyid Assadar da Alburujardi da Asshirazi da Alkazwini da Aldibadiba’i da Abu Harith Alyasiri da kuma Imam Khumaini, duka suna yin Mutu’a, kuma suna yin ta da yawa ba kadan ba!

Malamin shia:Eh wanan haka yake.

Dalibai: Na'am

Malamin shia:Akwai mai tambaya kafin mu ci gaba

Dalibai: eh mallam

Malamin shia: menene tambayan ku

Dalibai:Toh Mallam ko zaka bamu diyyar ka Suhaila muyi Mutu'a da ita ?

Malamin shia: A'a ba a mutu'a da yaran mu.

Dalibai:Toh mei yasa Mallam?

Malamin shia: saboda riwayan da  aka rawaito daga  Ahmad bin
Muhammad daga  Abu al-Hassan daga wasu daga cikin sahaban mu wanda  Marfu’u ne ga  Abu
Abdullah -alaihi salam- yace : “Karku kaskantar da Mumina da yin auren mutu'a da ita .” Wanan  Hadisin yana da isnadi Maqtu’u kuma yana da  Shuzouz a matanin sa .Abin da ake nufi a wanan riwayan shine cewa idan mace mumina wanda ta fito daga baban gida toh bai halata ba ayi Mutu'a da ita ba saboda zai zubar da mutuncin iyayen ta idan akayi Mutu'a da ita kuma ita ma mutuncin ta zai zube.  Kuma wanan zai zama Makruh ama kuma ba za a haramta ba .”
“Tahzeeb al-Ahkam” (7/253)

Dalibai: Kai?!

Malamin shia:kuna mamaki ne toh ga wata riwayan.  kuma daga gareshi daga  al-Hasan b. `Ali [Abu ‘l-
Hasan – a cikin at-Tahdheeb, Abu ‘l-Hasan `Ali – a cikin
al-Istibsar] daga daya daga cikin sahaban muhar zuwa ga Abu `Abdillah ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ.  Yace : Kar kuyi mutu'a da  mu’mina saboda zaku wulakanta ta .al-Hurr al-Amili  “Wasailu
shia” ( 21/26).

Dalibai: Toh mallam matsayin matan mu da naku mallamai akwai bambanci ne ?

Malamin shia: kwarai kuwa

Dalibai: Toh Mallam Ya Allah zai Halata wanan " Mutu'an" idan aikata hakan zai kawo kaskanci da zubar da mutuncin iyayen yarinyar da aka yi mutu'a da ita ?

Malamin shia:Allahu a'alamu .

Dalibai: Hmmmmmmmmmmmmmm!!!!!!!!!!!


A saurari ci gaba in sha Allahu Ta'ala.

ZAUREN FIQHUS SUNNAH 08034666220

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...