Skip to main content

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

Tambaya :
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta.

Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.


Amsa :
To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.


Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.


Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in" kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230.

 Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da Annabi Muhammad ya zo da shi" kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904. Kuma Albani ya inganta shi .


INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.


Allah ne mafi sani.


Dr Jamilu Zarewa
14\4\2014.

Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...