YANDA AKE SALLAN KISFEWAR RANA KO WATA A TAKAICE:
KIRAN JAMA'A:
Za a rinka maimaitawa kalmar "Assalatu Jaami'ah" har sai an tabbatar da jama'a sun ji, saboda hadisin Abdullahi Bn Amru dake cikin Bukhari da Muslim.
YANDA AKE YIN TA:
Raka'o'i ne guda biyu a kowace raka'a akwai tsayuwa biyu, da karatu biyu da ruku'u biyu da sujada biyu; ga bayaninsu kamar haka:
Raka'an farko liman zai kabbara ba tare da an tayar da iqama ba, sannan ya karanta fatiha da sura mai tsaho, sannan ya yi ruku'u mai tsaho, sannan ya dago daga ruku'u sai ya karanta fatiha da sura mai tsaho, amma kai ta kai na farko tsayi, sannan ya sake ruku'u mai tsaho amma kar ya kai tsayin ruku'u na farko, sannan ya dago daga ruku'u sai ya tafi sujada mai tsaho, sannan idan ya dago daga sujada sai ya sake komawa sujada mai tsaho amma karta kai na farko tsayi, sannan sai ya sake mikewa. Ya samu raka'a daya kenan, kuma haka zai maimaita a raka'a ta biyu.
Wannan shi ne bayani a takaice kamar yanda ya zo a hadisin Nana A'isha, Allah Ta'ala Ya kara yarda a gare ta, dake cikin littafin Sahihu Muslim.
Sannan yana daga cikin Sunnah idan an kammala wannan sallah, Limami ya umurci mutane da yawaita addu'a, tuba, da neman gafaran Allah Ta'ala. Kamar yanda Ya zo a cikin littafin Sahihul Bukhari.
Allah Ta'ala Ya sa mu dace.
Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
ZAUREN FIQHUS SUNNAH 08034666220
Comments
Post a Comment