ZAN IYA KARA GASHI, SABODA MIJINA ?
Tambaya :
Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi, don zaman auranmu ya kara dadi ?
Amsa:
To 'yar'uwa wata mace ta je wajan Annabi s.a.w. ta ba shi labari cewa : 'Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma gashi mijinta ya
umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta iya karawa ? sai Annabi s.aw. ya ce mata : A'a, saboda an la'anci masu kara gashi". Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4831.
Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa : bai halatta mace ta kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah .
Allah ne mafi sani .
Dr Jamilu Zarewa
22\4\2015.
Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH sai ya yi saving wannan number 08142082937 sannan ya aika da cikakken sunansa da adireshinsa.

Comments
Post a Comment