ZAN IYA NEMAN SAKI SABODA MIJINA BA
YA HAIHUWA ?
Tambaya :Don Allah malam na auri wani mutum,
amma har yanzu ba mu haihu ba, shin zan iya neman saki, don na ji an ce Annabi (s.a.w) ya ce matar da ta nemi saki ba za ta shiga aljanna ba ?
Amsa :
To Yar''uwa hadisi ya tabbata daga Annabi
(s.a.w) cewa : "Duk matar da ta nemi saki ba tare da wani dalili ba, ba za ta ji kamshin aljanna ba"
kamar yadda Abu-Dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2226.
kuma Albani ya inganta shi .
Wasu malaman sun tafi akan cewa mace za ta iya neman saki , idan ba ta san mijinta ba ya haihuwa ba, sai bayan sun yi aure, saboda wannan yana iya zama aibun da za'a iya raba aure saboda shi.
Duba : Sharhul-mumti'i 12/ 220.
Sai dai zai yi kyau kada ki yi gaggawar
rabuwa da shi, saboda a lokuta da yawa,
Allah yana iya jarrbar miji da rashin haihuwa, daga baya kuma sai Allah ya
warware masa ya bashi 'ya'ya .
Allah ne mafi sani.
Jamilu Zarewa
1\10\2015
Comments
Post a Comment