Wata rana Ibrahim Bn Adham, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama, ya zo wucewa sai ya ji wani mutum yana ta maganganu marasa amfani, sai Ibrahim Bn Adham, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama, ya tsaya ya ce da wannan mutumin:
Shin wannan maganganu da kake yi akwai wani lada da kake fata Allah zai baka sanadiyar su?
Sai mutumin ya ce: a'a
Sai Ibrahim Bn Adham, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama, ya sake tambayar shi ya ce masa:
Shin kana da tabbacin wadannan maganganu za su kare ka daga azabar Allah?
Sai mutumin ya ce: a'a
Sai Ibrahim Bn Adham Allah Ta'ala Ya yi masa rahama ya ce masa: "To me ya kai ka magana akan abun da baka fatan samun rahama ko kariya daga azabar Allah sanadiyar su?."
Don haka mu yi kokari mu kiyaye kalamanmu
Mu haɗu a fitowa ta 8 in sha Allahu Ta'ala.
Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria

Comments
Post a Comment