Assalamu Alaikum.
To Allah ya gafarta malam, wanda ya san wajibcin sallah da azumi akansa amma saboda ya taba jin fatawar cewa duk wanda yasha giya sai yayi kwana 40 ba'a ansar ibadar sa shi kuma baya kwana 40 baisha giya ba sai yabar sallah da azumi tsawon shekaru, yanzu kuma ya tuba ya bari ya ramuwar sallar da azumin da yabari zai kasance?
Wa'alaikumussalam
Amsa
Lallai hadisai sun nuna ba'a karbar sallar wanda ya sha giya ta kwana arba'in kamar yadda yazo cikin silsilah swahiha 709, hadisin ya nuna idan mutun ya tuba Allah zai yafe masa, saboda haka tunda ya tuba muna fatar Allah zai yafe masa, sai yaci gaba da istigfari da yawaita ibada,
Malamai sunyi sabani wajen ramakon sallah da azumi ga wanda yabar su baiyi har tsawo wani lokaci, wasu sunce zai rama wannan shine ra'ayin Jamhurun malamai waau kuma sunce ba zai rama ba don sun gina fahimtar su akan dalilai na shari'a da suka nuna kafurcin wanda yabar sallah, sannan suka ce in ance zai ya rama hakan ka iya wahalar dashi kila ya kasa ya koma gidan jiya, suna hujja kuma da fadar cikin Suratul Ɗaha 11, da ta 82.
Don haka dai babu ramuwa akan sa sai istigfari da tsaida sallah da ci gaba da azumi da lazimtar ibada sosai da sosai, an tambayi malaman lajna 6/41 hukuncin wanda yabar sallah da azumi sun bada fatawar ba zai rama ba.
Wallahu A'alam.
Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
07/08/2016.
Daga : ZAUREN FIQHUS SUNNAH group.
Comments
Post a Comment