Tabbas mata mutane ne masu mutumci ba mai mutumta su sai mutum mai mutumci, kuma ba mai wulakanta su sai wulakantacce. Annabi (saw) ya mana wasiyya a ranar Hajjin ban kwana kan tausasawa mata, da kuma umarni ga maza da mta su kula da hakkin junan su.
To 'yan uwa na maza da mata mu sani yana daga hakkin iyalan mu akan mu lallai mu kula da tarbiyyar su, sannna a junan mu musulmai muna yiwa juna nasiha, bisa wannan nake tuna mana cewa: Allah yayi umarni ga Annabi (saw) da ya gayawa matansa, da 'ya 'yansa, da sauran mata muminai kcewa in zasu fita su sanya sutura isash-shi ya da zata rufe masu dukkan jiki. Anan kada mu bari al'adun mu, ko zamani ko tasirin wayewa yasa mu manta da umarnin Allah dana manzon Allah yayin sanya suturar mu.
Shifa bawa mabukaci ne a gun Allah, kuma ba sai lokacin bukatar mu a gun Allah ba, ko yayin wani taro na addini, ko yayin jana'iza ko in za'a je ta'aziyya, ko ranar sallah ko a haduwar junan mu zamu yiwa Allah da'a ta sanya suturar da aka umarce mu ba.
Na kan ga 'yan uwa mata yayin bukukuwa, ko a manyan makarantu, ko in sunyi nesa da gida, ko ofisoshi suna sa6awa Allah wajen tufafi da yakamata su saka... Lallai wannan babban laifi ne. Mu Sani a ko ina muke Allah yana ganin mu, kuma kowa a lahira da aikin sa za'a masa hisabi, muji tsoron Allah bamu san akan wacce ga6a zamu bar duniya ba..
Lallai iyaye, malami da shugabanni ku tsaya kan al'ummar mu da nusar damu kan tsarin suturar da wassu matan mu na yau ke sawa in zasu bayyana a gaban jama'ar da bai halatta su gansu da irin wannan tufafi ba.
Hakika bayyana tsiraici haramun ne, kuma yana haifar da matsaloli da yawa. Allah ya hana fita irin ta kafirai, da sanya matsats-tun tufafi, da son yin kama da maza, ko koyi da arna.
Matan dake bayyana tsiraici basa tsoron gamuwa da fushi Allah, ko tunanin hatsarin gamuwa da shafar aljanu, mu sani fa 'yan uwa mata bayyana jiki yana jawo raguwar imani da zubewar mutumci, da bushewar zuciya da karancin kunya, kuma zuriyar ku zasu iya gadon wannan mugun aiki, hakanan al'umma na iya koyi daku.
Allah mai rahama mai jin kai muna rokon ka shiryar da iyalan mu, Ka sanya matan al'umar mu manya da yara suna sanya sutura wanda ka yarda da ita, Allah ka yafe masu kura-kuran su, ka sanya kwadayin rahamar ka a zukatan su, ka tsare su daga fizga daga shaidan.
Mata ku sani kune iyayen al'umma kuma kune makarantar farko ga 'ya 'yan ku. To fa ance in bishiya ta karkace bata bada mikakkiyar inuwa.... Muna fatan ku zama na kwarai al'umar mu su taso a hannun mata masu nagarta.
Daga:
Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa
Comments
Post a Comment