Sutura adireshi ce ga dan Adam. Da ita ake gane girman hankalinsa ko tawayar tunaninsa.
Haka kuma sutura ita ce babbar ni'imar da Allah ya rabe mu da ita daga sauran halittu.
A lokacin da kakanmu Annabi Adam (AS) ya saba ma umurnin Allah shi da matarsa sai Allah ya bayyana fushinsa ya tsiraita su.
Bisa ga haka, idan ka ga dan Adam a tsiraice, ko kamar a tsiraice, namiji ne ko macce to yana cikin fushin Allah.
Shugabanmu Baba Buhari da sauran manyanmu muna kira ku ji tsoron Allah, kada ku ko iyalanku su ja mana fushin Allah. Musamman ku tuna ku da matanku duk abin koyi ne. Har yau a Najeriya ba mu daina koken Stella style da matan Arewa da ya'yansu mata suke yi ba.
Allah ya shirye mu, mu da shugabanninmu baki daya.
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto
2 ga Zul Qi'ida 1437H
5th August 2016

Comments
Post a Comment