Skip to main content

SIFFOFIN MACE SALIHA (4)

Wallafar: Shaik Adamu Muhammad Dokoro (Gombe)

Fotowa ta 004

Suna daga cikin siffofi mace saliha:

18, MAI YADDA DA HUKUNCIN ALLAH: Da kuma ikonsa kamar yadda Manzon Allah Yace" Mamaki ga al'amarin mutum musulmi,al'amarinsa duka alherine,in farin ciki yasameshi sai yagodewa Allah sai yazama alheri agareshi,in ciwo yasameshi sai yayi hakuri hakan yazama masa alheri"(Imam Muslim) Allah Yace "inacika ladan masu hakuri batare da hisabi ba" Suratul Zumar ayata 10.

19, MAI MAIDA AL'AMARI GA ALLAH: Mai bauta ma Allah tare da komawa ga Allah koda shaid'an ya shafeta idan ta tuna tana komawa ga Allah Mad'aukakin sarki.

20, MAI JIN CEWA ALLAH ZAI TAMBAYETA:Iyalenta domin tambayar da Allah zaiwa mace kan iyalen gida yafi na miji saboda tafi namijin sanin abunda ya bayyana fa halayyar yara acikin gida.Manzon Allah ( ) Yace Mace za'atambayeta gidan mijinta da 'ya'yanta kamar yadda yakamata

21, *ABIN DA YAFI DAMUNTA* :Shine yardan Allah,Tafi damuwa tasami yardan Allah kamar yadda Nana A'isha ta ruwaito hadisi daga Manzon Allah( ) Yana cewa Wanda yanemi yardan Allah ya isar masa daga mutane,wanda yanemi yardan mutane da fushin Allah,Allah zai barshi da mutane (Timidhi)

22, TANA MISALTUWA DA BAUTAWA ALLAH: Mai shiryarwace ga maganarta,da tafiyarta,da suturarta da aurenta,da bukukuwanta da sauran al'amarinta duka sai abinda addini yafad'i bata sa son zuciya tayi bid'a ko shishshigi.

23, TANA AIKI DOMIN TQIMAKON ADDININ ALLAH:Bata fifita duniya akan addini,kamar yadda Allah Yace Ban halici mutum da aljan ba sai don su bautamin (zariyat ayata 56)

24, MABUWAYYIYA DA KANTA:Da addininta ba kamar yadda wasu suke basu wulakanta kansu kuma su wulakanta addinincsu,mumini girma nasa ne kuma Allah ne Ya basu domin bai yarda da kaskancin ba wato shi addini.

25, BATA JINGINA KANTA GA KOWA SAI ALLAH: Wato Allah shine majibincin al'amarinta da Manzonsa,ma'ana shine mai bata umarni sai manzonsa,sai kuma umarnin da yadace dana Allah da manzonsa kamar yadda yagabata.

27, MAI UMURNI CE DA KYAWAWAN AYYUKA: Kuma mai hani ce da munanan ayyuka kamar yadda Alkah Yace Muminai maza da mata masoyan juna ne,kuma suna umurni da kyawawan ayyuka suna hana munanan ayyuka(Tauba aya71) .Kenan mai wa'azi ce kuma mai ilimi ba jahila ba zata yi wa'azi kuma tana taimakawa mata 'yan uwanta wajen ilimantarwa,wa'azi,nasiha da sauran ayyuka na gari.

Allah Yasa muna daga cikin wad'annan mata salihan.(Amin)

A sauraremu a fitowa na 5 in shaa Allah.

✍🏻 'Yar uwarku a musulunci:
Ummu Abdillah Gombe
Repost
September 2016

UMMAHATUL MUMININ

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...