✍🏾Daga👇🏽
Dr. Muhammad Kabir Asgar
☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘
Al-Imamu Ahmad da Tirmiziy da Ibnu Majah da wasunsu sun ruwaito hadisi daga sahabi Ziyad Dan Labeed Al-Ansaariy (رضي الله عنه) ya ce: “Wata rana Annabin Allah (صلى الله عليه وعلى آله وسلم) ya ambaci wani zance sai ya ce: wannan zai faru ne a lokacin tafiyar ilimi. Sai na ce ya Manzon Allah! Yaya za a ce ilimi ya tafi alhalin ga Al-Qur’ani nan muna karanta shi, muna koya wa yaranmu har tashin Al-Qiyama? Sai Manzon Allah (وسلم صلى الله عليه وعلى آله) ya ce: Haba Ziyad! Kai da nake ganin ka kamar mai kan gado a cikin mutanen garin Madina! Ba ka ganin ga Yahudu nan su da Nasara suna ta karanta Attaura da Injila amma ba a aiki da abin da ke ciki?.”
Daga
ZAUREN FIQHUS SUNNAH /
MINBARIN SUNNAH
Comments
Post a Comment