BABU BANBANCI TSAKANIN SALLAR NAMIJI DA TA MACE!!!
Tambaya:
Assalamu alykum, Idan mata suna jam'in sallah shin
limamiyarsu zata jiyar dasu katarun fatiha da sura (awajen bayyanawa)?
zata bayyana kabbarori yadda zata jiyar da su?
kuma zasu hada qafafuwansu a sahu kamar yadda maza suke.
Amsa:
Wa'alaikum assalam, Babu bambanci tsakanin sallar mace da ta
namiji a zance mafi inganci, saboda babu nassoshi yankakku wadanda suka
bambanta, don haka in mace ta yiwa mata limanci za ta jiyar da su karatu kamar
yadda namiji yake jiyar da mamunsa maza, za su hada sawu saboda zukatansu kar
su saba.
Idan mace ta limanci 'yan'uwanta mata za ta tsaya ne a
tsakiyarsu, in har ya zama akwai maza a kusa wadanda ba muharramai ba, macen za
ta iya yin kasa da muryarta saboda kada su fitinu da ita.
Allah ne mafi sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
01/06/2016
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment