WUTIRI DA KAIFIYYARSHI
TAMABAYA
Asslm alkm, malam inada tambaya, ko yana halatta in ranka
wutri bayan ketowar alfijir, sannan wutri kashi nawa ne kuma yaya kaifiyyar su
take?
Amsa
Wslm Wrhmtlh Wbrkth
WUTIRI ana yinsane
daga bayan isha'i zuwa kafin ketowar alfijir, don Hadisinda ANNABI SAW cikin
ruwayar MUSLIM daga ABU SA'ID AL-KHUDRY yace👉🏼
أوتروا قبل أن تصبحوا
wato= kuyi wuturi kafin asubah,
Amma ga wanda
yamakarane ko yamanta yana iyayi koda bayan ketowar Alfijir don hadisin ABU
SA'AD ruwayar AS'HABUSSUNAN banda NASA'I, ANNABI SAW yace👉🏼
من نام عن الوتر أو نسيه فليصل إذا
أصبح أو ذكره
Wato= wanda barci ko mantuwa yasa wutiri yasubuce masa- yayi
koda asuba tayi,
Amma wanda ba
mantuwaba kuma ba makaraba yabari da gangan har alfijir yaketo to yayi asararsa
kawai,
Kuma ana iyayin
wutiri raka'a 5 ko 3 ko 1 yadda yazo a Hadisin ABU AYYUBAL ANSARY,
ALLAHU A'ALAM
Amsawa✍ Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
Daga
ZAUREN FIQHUS SUNNAH / MINBARIN SUNNAH
Comments
Post a Comment