Skip to main content

DOMINKI NE DA MIJINKI Daga Baban Manar Alqasim (Mace ta gari)

DOMINKI NE DA MIJINKI #1
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Rubutawar✍
Baban Manar Alqasim

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Babban abin da mai son jin dadin aure ya kamata ya lura da shi shi ne: Mace ta gari, ita za ta iya zama masa zinariya, duk lokacin da ta yi datti in aka wanke sai qyalqyalinta ya fito sarari, amma aure don kyau (wanda shi muke yi yanzu) kamar baqin qarfe ne da aka shafa masa kumfar zinare, yana daukan ido da ban sha'awa, da zarar ka yi amfani da shi Daya, Biyu qyalqyalin zai fita munin kuma ya bayyana, daganan ba sauran sha'awa kuma, galibi qyalqyal-banza dinnan su maza suka fi so, shi ya sa mai haja yake tallata musu don samun kasuwa, maganar gaskiya duk wani dan kasuwa riba yake nema.
Mace ta gari za a same ta da:
1)KAMEWA, daga duk wani abu da zai sosa wa maigidanta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
2)GASKIYA, in za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.
3)ZA'BIN MIJINTA A KANTA, tana buqatar abu amma in baya so za ta barshi, ko ta yi don shi yana so koda kuwa ba ta so.
4)AMINCEWA, duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.
5)TAWALU'U, ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah RA da Annabi SAW.
6)NATSUWA, kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.
7)KUNYA, ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
8)KWANCIYAR HANKALI, mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
9)GODIYA, duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.
10)HAQURI, a kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa)
11)TSAYUWA QYAM, a wajen bauta da qarfafa mijin da 'yansu.
12)AMANA, ta zama mai amana, kar ta yarda maigidanta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.
13)CIKA ALQAWARI, yana Daya daga adon mace da namiji.
14)TSORON ALLAH, a duk abin da za ta yi.
15)DANNE ZUCIYA, yayin da aka baqanta mata rai.
Wadannan abubuwa guda 15 su suke nuna mace ko miji nagari, kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba.
TO MUN FA FARA.

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...