DAGA ZUCI ZUWA ZUCI
Makarantar rayuwa; kowa da ajinsa
Daga: Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah ✍
13th Almuharram, 1441H
13th Satumba, 2019M
Ɗazu da safe Babban Malami Dr. Mansur Sokoto ya turo min
wani rubutu cikin yaren Ingilishi mai taken: life is a class of one a
ciki marubucin yana bada labarin wani biki da ya halarta na ƴar ɗaya daga cikin
abokan karatunsa a jami'a, shekaru talatin da suka wuce, sai ya haɗu da wasu
abokan karatun nasa, a nan ne ya ga yadda Allah mai iko ya banbanta rayuwarsu,
a inda wasu sun fi wasu a wani fage, wasu kuma sun fi su a wani fagen, sai yake
gane cewa: za ku iya yin makaranta ɗaya da mutum, kuma aji guda, amma a
makarantar rayuwa ajinku ba guda ba
- Kana iya fin 'dan ajinku 'kwa'kwalwa shi kuma ya riga ka
samun aiki.
- Kana iya rigarsa samun aiki ya riga ka aure.
- Yana iya rigarka samun aiki ka zo ka wuce shi a matsayi.
- Yana iya wuce ka a matsayi kai kuma ka fi shi shahara a duniya....
Wannan duk yana cikin tsarin Allah Buwayi Gagarerren Sarki.
Saboda haka:
- Ka zama mai yarda da ajin da Allah ya aje ka bayan ka yi
abin da za ka iya yi na motsi, da kaiwa da komowa.
- Ka rik'a kallon ni'imomin da Allah yai maka, ta haka za ka
iya gode masa.
- Ka rik'a dubi zuwa ga wad'anda ka wuce su ba wad'anda suka
wuce ka ba.
- Ka fahimci ita rayuwa kamar zanen ziza take, lauye-lauye
gare ta.
- Gane haka na saka ka zauna lafiya da Ubangijinka(Allah),
da zuciyarka, da jikinka, da mutane gaba d'ayansu.
Allah ya saka ma wancan mai rubuta, da Dr Mansur mai turawa,
da alkhairi.
Allah ya bamu ikon fahimtar irin wad'annan nau'ukan
tsinkaye, da kuma aiki da su.
Na bar ku da wannan.
Comments
Post a Comment