Skip to main content

Muhimmancin Lokaci A Rayuwar Musulmi daga Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Fatawowin Rahma

Shimfida: Muhimmancin Lokaci A Rayuwar Musulmi

Tambayoyin da ke ciki-

1. Tsokaci akan auren bazaura, ko auren wadda take wata qabila.

2. Mafita ga wanda ya yaudari budurwa da ya so ya aura duk da ya bata haquri amma taqi yafe mashi!

3. Hukuncin iyayen da su ka kashe dansu da gangan.

4. Rama azumi farilla tare da niyyar samun ladan azumin nafila, ko falalarta.

5. Zakkar manomi da ya ranto kudi domin amfani da kudin a nomansa.

6. Mamun da ya manta karanta suratul fatiha a sallar farilla.

7. Mutumin da ciwon hassada ya dame shi duk da yana yaqi da zuciyarsa akan cutar hassadar da ke adabar shi.

8. Shin akwai azumin kaffara ma mutum da ya ajiye motorsa (parking) sai wani ya dake shi sakamakon hakan ya daki wani yaro har ya mutu.

9. Ya hallata mai saya da sayar da motorci yayi ciniki motor har ya karbi wani bangare na kudi motar da bai mallaka a lokacin cinikin ba?
10. Hukuncin cakuduwar dalibai maza da mata yayin shiga motar makaranta.

11. Ya hallata mace ta bi sallar jum’a daga gidanta?

12. Mutumin da in an ba shi aika yake qara kudi akai saboda samun sauki farashi a inda ya ke sayo kayan. Shin ya lallata abında ya ke ci?

Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...