Skip to main content

NASIHAR WATA UWA MAI HANKALI GA 'YARTA YAYIN AURENTA

NASIHAR WATA UWA MAI HANKALI GA 'YARTA YAYIN AURENTA

1 - Ki zama kamar baiwa ga mijinki, sai shima ya zama kamar bawa a gare ki.

2 - Kada ki nisance shi, sai ya manta dake.

3 - Ki kiyaye masa hancin sa,jinsa, da ganinsa; kada ya shaki wani abu daga gareki sai
mai qamshi kada yaji wani abu daga bakinki sai mai dadi kada yaga wani abu daga gareki sai mai kyau.

4 - Ki kiyaye masa lokacin Abincin sa da lokacin Baccin sa, domin yunwa tana hassala mutum, kuma gurbata masa bacci na fusata shi.

5 - Ki kiyaye masa Dukiyar sa,dangin sa da gidan sa, domin suna da matukar muhimmanci a gareshi.

6 - Ki guji yin farin ciki yayin da yake cikin bacin rai, kuma ki kiyayi yin bakin ciki, yayin da yake farin ciki.

7 - Ki girmama shi matuqa shima zai girmamaki matuqa, fiye da yadda kowa zai girmamaki.

8 - Ki sani cewa gwargwadon yadda kike amincewa da ra'ayin sa gwargwadon tausayawar da zai miki.

9 - Kada ki juya masa baya yayin da ya kusanto gareki.

10 - Ki sani yake 'yata baza ki sami yadda kike soba har sai
kin zabi yardar sa akan yardar ki, kin fifita son ransa akan son ranki.

11 - Kada ki fiya naci ko fushi a lokacin da kike neman wani abu agareshi, sai ya kosa dake.

12 - Daga karshe don girman Allah ki yi hakuri ki zamo shimfida ga mijinki zai zamo rumfa a gareki.

ALLAH YASA SAURAN YAN UWA MATA SUMA SUYI AMFANI DAWAN NAN NASIHA.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...