WASU ABUBUAWAN DA SUKE YAYE BALA'I, DAMUWA DA DUK WANI
Tsanani DA MUTUM YA TSINCI KANSA A CIKI......
Daga
Sheikh Dr. Sani Umar R/Lemo
1. Kyautata imani da Allah da nisantar abin da yake tauye
imani: Allah ya yi alkawarin taimakon bayinsa muminai, da ba su nasara akan
abokan gabarsu. Don haka matukar akwai imani da Allah a zukatan bayi to Allah
ba zai tozarta su ba.
2. Tuba da Istigfari da komawa zuwa ga Allah.
3. Yawaita ayyuka na kwarai, saboda ayyukan kwarai sukan
kawo wa zuciya nutsuwa, kamar yadda munanan ayyuka sukan kawo wa zuciya bakin
ciki da damuwa da kunci.
4. Yawaita Sadaka: musammam ma a boye ba tare da an sani ba,
ya tabbata a hadisi Manzon Allah S.A.W ya ce “Aikata kyawawan ayyuka suna kawar
da munanan abubuwa, sadakar boye tana kawar da fushin Ubangiji, sada zumunci
yana kara tsawon rayuwa, dukkan aikin alheri sadaka ne, masu aikin alheri a
duniya, su ne ma’abota alheri a lahira, masu munanan ayyuka a duniya, su ne
masu ma’abota mummuna a lahira, farkon wadanda za su shiga Aljannah su ne masu
aikata kyawawan ayyuka”.Dabaran i ne ya rawaito shi. .
5. Addu’a: ba don addu’a ba da mutane da yawa sun halaka.
Allah madaukakin Sarki yana jarrabar bayinsa da bala’i don su koma gare shi, su
kaskantar da kai da addu’a, idan suka koma zuwa gare shi, suka kasakantar da
kai sai ya yaye musu. .
6. Umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna: Allah ba zai
halaka al’umma ba, matukar akwai masu umarni da kyakkyawan aiki da hana
mummuna. .
7. Nisantar Zalunci : Allah ya halakar da al’ummu da yawa
saboda zalunci. Mafi girman zalunci shi ne shirka da kafirci, sai zaluntar
bayin Allah a cikin dukiyarsu da mutuncinsu da jininsu, mu nisanci zalunci mu
zauna lafiya. .
8. Zikiri wato ambaton Allah, da baki da zuciya da gabbai.
Da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa.
Allah ya yafe mana kurakuranmu. Allah ka amshi tubanmu.
Amin.
Comments
Post a Comment