Skip to main content

IDAN KA SAKI MATARKA, BAN YAFE MAKA BA !! by DR. JAMILU YUSUF ZAREWA


Tambaya

Assalamu alaikum.
Idan uba yace wa Dan shi kar ya sake matar sa, in ya sake ta bai yafe ba. Toh idan yaron ya sake ta yana da laifi ne a wurin Allah?
Yaron auren dole aka masa da matar, kuma matar ta ki zama a gidan. ba su ma taba hada shinfida ba, gashi baban shi ya gargade shi kar ya sake ta ?.


Amsa

Wa alaikum assalam, matukar Manufofin zamantakewar ba za su tabbata ba in su ka cigaba da zama tare ya halatta ya sake ta,  saboda cigaba da rike ta sabon Allah ne, biyayya ga Allah tana gaba da biyayya ga Iyaye.

Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta (229) "Saki karo biyu ne,  bayan haka kuma sai a rike ta da kyautatawa ko kuma a rabu cikin lalama", a aya ta (230) Allah ya halattawa mace ta fanshi kanta in ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokin aure ba, Idan suka rabu Allah zai azurta kowa daga falalarsa kamar yadda ya zo a Suratun Nisa'i .

Daga cikin Manufofin aure akwai samun Zuriyya da nutsuwa da kuma debe-kewa, rintse ido daga kallon Haram, mutukar Manufofin suka goce saki yana halatta.
Ba duk mummunar addu'ar iyaye Allah yake amsawa ba, in da Allah yana amsa duka munanan addu'o'in mutane da sun mutu Miris, kamar yadda Allah ya yi bayani a Suratu Yunus aya ta (11).

Allah ne mafi sani

Amsawa✍🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

29/09/2019

Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...