Tambaya
Assalamu alaikum malam tambaya dan Allah malam kamar wanne aikine take bata sallah kai tsaye
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ayyukan da suke bata sallah suna da yawa, daga ciki: akwai dariya Sannnan yawan motsi da soshe-soshe yana bata sallah a wajan wasu malaman, magana wacce ba ta gyaran sallah ba na daga cikin abububuwan da suke bata sallah.
Yin tusa ko fitsari ko cin abinci ko abin sha suma suna ciki. duk abinda yake bata alwala yana bata sallah
Allah ne mafi sani
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment