Tambaya:
Assalamu Alaikum mallam dan Allah an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi?
Amsa
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .
Allah ne mafi sani.
Dr.Jamilu Yusuf Zarewa
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment