Ana samun daɗin zaman aure da abubuwa kamar haka :
1- Addini : mai kiyaye dokokin Allah a komai.
2- Kyawun hali : don in ba kyan hali za a cutu.
3- Kyawun halitta : zai fi kauda idon mutum daga wasu matan.
4- Arhar sadaki : Umar R. A yace kar ku sa sadaki mai tsada sosai. Kuma malamai sun ƙyamaci miji ya sa ido a kuɗin mace, Sufyan As-Sauri yace : in ka ji mutum na tambayar me mace ke da shi na kuɗi ɓarawo ne.
5- Budurci : An fi son mace ta zama budurwa, ta fi bazawara son miji, shima miji ya fi son budurwa.
6- Mai haihuwa : A kan tsani macen da ba ta haihuwa.
7- Yar manya: gidan tarbiya da addini.
8- Ta zama 'yar wani dangi : ma'ana auren da ba na zumunci ya fi na zumunci.
Kuma shima miji an so ya zama nagari mai addini, in ba haka ba mace za ta sha wuya, wani mutum ya tambayi Hassan Al-basary, wa zan aura wa ɗiya ta ? Sai yace mai tsoron Allah, don in yana son ta zai mutunta ta, in bai son ta kuma ba zai zalunce ta ba.
Daga Abu Ahmad Tijjani Haruna
Comments
Post a Comment