Skip to main content

HANYAR SAMUN WADATA // 1

Babban abin neman kowane 'dan Adam a duniya itace hanyar da zai bi ya samu wadata cikin duniyar nan, wadata na iya daukar ma'anar rabuwa da talauci,dukkan wanda ke cikin talauci tabbas ba ya cikin wadata, wanda kuma yayi nasarar rabuwa da talauci haqiqa ya samu wadata.

Sanin haqiqanin menene Talauci, da Nau'ukanshi, da Sabubban da ke kawo Talaucin, da abubuwan da ke dawwamar da shi, da hanyoyin rabuwa da Talaucin, sune ababen da za su samar wa mutum da wadata. Wannan taqaitaccen rubutu ne da zai qunshi bayanai kan wadannan abubuwa kamar yadda na lissafo, domin bada gudunmawa ga talakawa su samu hanyar fita daga cikin talauci, masu wadata kuma kar su fada cikin shi, musamman kuma na yi rubutun ne domin amfanar da 'yan uwana 'yan Najeriya kuma 'yan Arewa da aka fitar da rahoton cewa su ke da kashi wurin tamanin na talakawan Najeriya.

MENENE TALAUCI ??

ANCE : Talauci shine rasa abubuwan buqatar da amfani da su ya zama dole a rayuwa, kamar gidan zama, suturar sanyawa, abincin ci, abin hawa ko kudin samun na haya.
Kuma ance : 
Talauci na nufin rasa mafi qarancin abinda masu matsakaiciyar rayuwa ke da shi. matsakaiciyar rayuwa itace abinda ake kira da rufin asiri a cikin al'ummarmu ta Hausawa.
Kuma ance : 
Talauci na nufin yin rayuwa cikin rashin lafiya (da zai gagari mutum yin maganin shi) da rashin abinci, da jahilci ( rashin ilimi) da kuma yawaitar mutuwar qananan yara saboda cututtuka.

Idan muka dubi wadannan ma'anoni za muga cewa duk kana iya maida su kan na farko, kenan muna iya cewa : 
Talaka shine wanda ya rasa buqatun dolen rayuwa. Idan muka kalli Talauci da Talaka da wadannan ma'anoni lallai za mu yadda a Arewacin Najeriya akwai talauci da talakawa masu yawan gaske, kuma su suka fi yawa.

NAU'IKAN TALAUCI/KASHE-KASHEN TALAUCI.
Duba da yanayin ma'anar da na ambata ta talauci, yana da kyau ka san cewa talauci ma iri-iri ne, ya danganta da yanayin yadda aka kalleshi. Misali in ka kalli girman rashin da talakawan ke ciki za ka iya kasa Talaucin kashi biyu : 
A- BAQIN TALAUCI : Shine ya zama mutum bai mallaki komai na dolen rayuwa ba, bai da wurin zama koda na haya ne, ba abinci ba ruwan sha mai kyau da sauran ababen dolen rayuwa.
B- MATSAKAICIN TALAUCI : Shine ya zamana mutum bai samun dolen rayuwa daidai da matsakaicin mai arziki(mai rufin asirin) inda yake rayuwa, sai dai kasa da shi.

In kuma ka kalli talauci ta fuskar samu da amfani da abinda aka samun, kana iya kasa shi zuwa : 
A- Qaramin Talauci : ya zama kana samun wadataccen abin rayuwa amma kana kashe su ta hanyar shirme da almubazzaranci da rashin sanin ya kamata.
B- Babban Talauci : ya zama ba ka samun ababen dolen rayuwa, tamkar dai bayanin da akayi kan baqin talauci.

Akwai wasu kashe-kashen talaucin, idan ka dube shi ta hanyar ababen da ke zama musabbabin talaucin, kamar : 
1- Talaucin da yanayi ke haifarwa, kamar ibtila'i ko rashin lafiya ko gobara ko kace karayar arziki.
2- Talaucin gado, kamar in ya zama iyaye da kakannin mutum sun rayu cikin talauci, shima haka na dauwamar da shi cikin talaucin.
3- Talaucin birni, sakamakon yanayin rayuwar birni na iya sa mutum ya zama cikin jerin talakawa, saboda tsadar rayuwar birni da kuma tsadar kayan masarufi, qila da qauye yake, samun shi ya isa ya kai shi jerin masu rufin asiri.
4- Talaucin qauye, yanayin rayuwar qauye kan iya sa mutum shiga jerin talakawa saboda qarancin hanyoyin samu.

Wadannan sune nau'ikan talauci, rubutu na gaba zai kawo bayanin ababen da ke kawo talauci.

Abu Ahmad Tijjani Haruna
24/02/2020

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...