SABUBBAN TALAUCI :
Idan ka dubi nau'ikan talauci da kashe-kashensu da nayi bayani a rubutun da ya gabata, yin nazari kansu zai iya sa ka fahimci me ke kawo talauci, domin kowane irin talauci za kaga kaman tare yake da sababin shi. In ka lura da kyau kana iya kasa sabubban talauci zuwa gida hudu a dunqule.
1- Sababin da mutum ne ya jawo ma kanshi.
2- Sababin da shuwagabanni ne suka jawo ma mutane shi.
3- Sababin da Allah ne ya qaddaro ma mutane shi.
4- Sababin da ya hada matsalar shuwagabanni da kuma su mutanen da ake shugabanta din.
Idan ka fahimci me ya jefa ka cikin talauci cikin sauqi za ka iya maganin shi, in kuwa ba ka fahimci ta ina ka shiga talauci ba za ka mutu cikin talauci, misali in ka fahimci kai ka jawo ma kanka talauci sai ka gyara kurenka, in kuma shuwagabanni ne suka ja maka sai kayi qoqarin zabar na gari idan zabe ya zo, in kuma qaddare ne talaucin ka, kayi Imani da qaddara ka ji tsoron Allah sai ya baka mafita, in kuma matsalar talaucin mutane da shuwagabanni ne su ka hadu aka shigar da mutane talaucin shima dai daukar matakin zai yi sauqi sosai.
Idan muka duba abubuwan da ke kawo talauci dalla-dalla, za su iya kai abubuwa kamar sha biyar (15).
1- RASHIN AIKIN YI : dole ne duk mai son rabuwa da talauci ya zama yana da aikin yi wanda ya dace da zai samar mai da wadata.
2- RASHIN ILIMI : ilimi ya qunshi ilimin addini da na zamani da na sana'a, jahili ba zai taba samun wadata ba, amma ka fahimci cewa karatu fa daban ilimi daban.
3- RASHIN IYA SARRAFA ABINDA KA SAMU : Idan ka zama baka iya amfani da abinda ka samu yadda ya dace ba, ka zama mai almubazzaranci ko wauta to lallai kana fadawa talauci.
4- BASHI : yawan cin bashi da rashin hakura da qoqarin amfani da abinda ke hannunka sau da yawa yakan jefa wasu talauci.
Wadannan abubuwan guda hudu (1-4) mafi yawancin mutane su ke jafa kansu a cikinsu.
5- LALATATTUN MASU MULKI : idan har inda kake rayuwa babu shuwagabannin da suka dace su shugabanci al'umma, kamar su zama ba su da siffofin da ake so mai mulki ya samu ko su zama azzalumai to tabbas mutanen su za su shiga talauci kuma za suyi nesa da wadata.
6- LALATACCEN TSARIN MULKI : ko da shuwagabanni sun zama na kwarai idan ba tsarin mulki ingantacce, ko kuma shuwagabannin basu iya gudanar da mulki ba tabbas jama'arsu za su tsinci kansu a halin talauci da rashin wadata.
7- CIN HANCI DA RASHAWA : duk al'umma da cin hanci da rashawa ta yawaita a cikinsu da wahalar gaske ace sun kubuta daga talauci.
8- RASHIN KAYAN MORE RAYUWA : A zamanin nan, garin da ya zama ba abubuwan jin dadin rayuwar mutane tabbas mutanen garin za su riqa shiga halin talauci rashin wadata, kamar inda ruwa mai kyau(famfo ko makamantanshi) ya ke wuya, rashin wutar lantarki da hanyoyin motoci da makamantansu.
wadannan hudun kuma (4-8) kana iya jingina su ga shuwagabanni.
9- ANNOBAR CUTUTTUKA KO FARI: duk lokacin da annobar cututtuka tazo, neman magani da jinya da rashin kwanciyar hankali kan iya sabbaba wa mutane matsalolin da za su iya shigar da su talauci, haka ma fari na rashin ruwa ko saukar wasu tsuntsaye ko fari kan iya haifar da qarancin abinci da yunwa.
10- HAUHAWAR FARASHI : idan farashin abubuwan da jama'a ke dolentuwa zuwa ga buqatarsu ya hau, tabbas hakan zai jefa su cikin rashin wadata da talauci.
11- TSANANTAR WANI YANAYI : misali damuna in ta wuce lokacin da ake tsammani amfanin gona zai lalace a samu qarancin shi, manoma ba za su samu ribar noma ba, gari kuma ba abinci, hakan zai kai mutane ga matsanancin yanayin talauci.
12- YUNWA : Idan yunwa ta sauka cikin al'umma tabbas sukan shiga mummunan halin rashin wadata da talauci.
Su kuma wadannan hudun(9-12) qaddarar Ubangiji ce ke kawo su.
13- TABIN HANKALI : duk da akwai na halitta, amma yawancin mutane kan bada gudunmawa sosai haka ma shuwagabanni wurin yawaitar masu tabin hankali wanda kuma shima yana daga cikin abinda ke sabbaba talauci. Asiri da tsafe-tsafe, da sakacin gwamnati na rashin samar da cibiyoyin maganin tabin hankali, da Imani da duk wata cutar tabin hankali aljanu ne sababinta, yana qawo yawaitar masu tabin hankali. mai tabin hankali kuma ba zai iya fita daga talauci ba, balle ya taimaki wani ya fita.
14- RIKICE-RIKICE DA TASHIN HANKALI : Idan tashin hankali da fadace-fadace da yaqe-yaqe suka yawaita a gari ko yanki ko qasa to dole a samu talauci da rashin wadata a wurin, rashin adalcin shuwagabanni da jahilcin mazauna gari na daga cikin ababen da ke haifar da tashe-tashen hankula.
15- YAWAN AIKATA SABO : sabon Allah da aikata ababen da ya hana na daga cikin mafi girman abinda yake haifar da talauci da rashin wadata. Idan mutane ba su bin dokokin Allah za su lalace kuma shugabanninsu ma za su lalace, kuma Allah zai jarabasu da ababe kala-kala.
wadannan na qarshe kuma (13-15) gwamnati da jama'a ne musabbabansu.
rubutu na gaba Insha Allahu zai kawo hanyoyin magance talauci da samun wadata.
Abu Ahmad Tijjani Haruna.
25/02/2020.
Comments
Post a Comment