HANYOYIN RABUWA/MAGANCE TALAUCI.
Talauci dai kamar yadda muka gani, sanin sabubbanshi shi zai taimaka wajen sanin hanyoyin da ya kamata a bi wurin yin maganinshi. Kamar dai sabubban, hanyoyin maganin ma za ka iya kasa su a dunqule kashi uku, a irin yadda na kawo a rubutu na biyu.(Mutane, Gwamnati, da kuma Allah SWT) A dalla-dallance kuwa :
1- SAMAR DA AIKIN YI : wajibi ne gwamnati ko daidaikun jama'a su samar da aikin yi ga marasa aikin yi, ko kuma mutum shi a karan kanshi ya nemi abin yin da zai samar masa ababen dolen rayuwa, mai zaman banza dole ya shiga talauci kuma ya shigar da wani, haka nan akwai masu kama da 'yan zaman banza, sune wadanda suka gama karatu suna jiran gwamnati ta basu ayyuka, ya kamata. Amma fa in ba na gwamnati ka tashi ka nemi naka.
Qarqashin samar da aikin yi, musamman a gwamnati ko ma'aikatu masu zaman kansu akwai muhimman tsare-tsare da za su taimaka wajen rage ma jama'a talauci, zan kawo su a dunqule ba tare da sharhi ba.
a- daidaiton albashi a dukkan ma'aikatun gwamnati.
b- qoqarin biyan ma'aikata mafi qarancin abinda mai rufin asirin cikin al'umma zai iya rayuwa a kanshi. Qaranci # 22, 000 a wata.
c- biyan kudin sallamar aiki, ko kudin hutu, ko biyan albashi lokacin da ma'aikaci ke ciwo.
d- tsarin aiki da zai ba ma'aikata damar yin aikinsu da kyau cikin nishadi, kuma ya bada damar daukar ma'aikata da yawa.
2- SAMAR DA MAKARANTU, DA CIBIYOYIN KOYAR DA SANA'O'I : Gwamnati da jama'a da qungiyoyi masu zaman kansu in suka samar da makarantu ingantattu da kowa zai iya shiga da cibiyoyin sana'o'i da kowa zai iya biya ya shiga ko na kyauta, zai taimaka sosai wurin rage talauci.
3- SAMAR DA INGANTATTUN CIBIYOYIN KIWON LAFIYA : samuwar wadannan ababe yadda kowa zai iya amfanuwa da su, su zama masu yawa kuma da sauqi, zai sauqaqa ma jama'a matsalolin lafiya da kan qarar da duk samun su da kwanciyar hankalinsu wurin neman magani. Hakan kuma in har ya samu zai rage talaucin jama'a sosai.
4- RAGE DOGON BURI DA MUNANAN BUQATU : dogon buri da buqata da suka fi qarfin samunka, za su sa ka yawaita cin bashi wanda kuma hakan zai jefaka talauci mai zafi. Rage wannan hali da wadatuwa da abin hannunka zai baka kwanciyar hankali da wadata.
5- SAMAR DA GIDAUNIYOYIN TALLAFI DA AGAJIN GAGGAWA : al'umma da gwamnati yana da kyau su riqa tallafa wa marasa qarfi da marayu da wadanda ibti'lain yanayi, ko hatsari, ko gobara, cututtuka da makamantansu ya fada mawa, yin haka zai bayar da gudunmawa babba wurin magance talauci da samar da wadata cikin al'umma.
6- TSAYARWA DA ZABAR SHUWAGABANNI NA GARI : duba mutanen kirki masu dukkan siffofin shugaba da tsayar da su takara da zabansu zuwa kan madafun iko da gudanarwa zai kawar ma mutane talauci ya kawo musu wadata.
7- SAMAR DA KYAKKYAWAN TSARIN GUDANARWA : A ko ina jama'a suke karkashin wani jagoranci in ba kyakkyawan tsari haqiqa wannan jama'a za su iya shiga kowane irin hali mara dadi, amma in akwai tsari komai nasu zai kyautata kuma za su samu wadata.
8- SAMAR DA SHIRYE-SHIRYE DA CIBIYOYIN BADA SHAWARWARI DA WAYAR DA KAI : wasu kamar yadda ya gabata rashin sanin tsarin gudanar da rayuwarsu ne ke jefa su a talauci, idan aka samu cibiyoyi irin wadanda za su riqa fadakar da jama'a kan hanyoyin gudunar da rayuwa da tattali, da haka sai kaga jama'a sun rabu da talauci sun wadatu. Hatta mutum a karan kanshi in ya zama mai neman shawara da wayewar kai ba zai fada talauci ba.
9- HADIN KAI : Babban matakin yaqar talauci ne, yana hana Hassada, gaba, son kai, wanda duk suna haifar da rikice-rikice cikin al'umma, shi kuma rikice rikice cikin al'umma na haifar da talauci, hadin kai da zaman lafiya kuma na kawo wadata.
10- BIN DOKOKIN ALLAH ( UMARNI DA HANI) bayar da zakka da yawaita sadaka da kyauta, da barin cin riba, da barin cin hanci da rashawa, da nisantar duk wata hanyar cin dukiyar jama'a ba da haqqi ba, hanyoyi ne da musulunci ya zo da su don magance talauci. Haka nan a qarqashin wannan gabar nisantar duk sabon da ke jawo fushin Allah SWT har ya jarabci mutane da Ibtila'i zai haifar mana da arziki da wadata mai dorewa.
Wadannan hanyoyine goma da in har aka bi su na tabbatar za a samu WADATA.
Rubutu na gaba na qarshe zai kawo abubuwan da ke hana fita daga talauci.
Abu Ahmad Tijjani Haruna
26/02/2020.
Comments
Post a Comment