1- koyar da su tsoron Allah da ganin girman saba mishi da illolin sabon.
2- kulawar iyaye ga 'ya'yan ta hanyar sanin shafukan da suke ziyarta ko yaushe, ta hanyar binciken wayoyin ko ta wasu hanyoyin zamanin.
3- shagaltar da lokutansu da ababe masu mahimmanci na ilimi da ibadu.
4- kulawa da sanin abokan da suke hulda da su a intanet da kuma zahiri.
5- nuna musu illolin shafuka masu hatsari a intanet, kamar shafukan batsa, da caca, da koyon sata ta intanet.
6- Tattaunawa da su don sanin ababen da ke burgesu ko bata musu rai da basu haushi a intanet.
7- samar musu abinyi a kan intanet da nuna musu shafukan da ya dace su mu'amalanta da wanda bai dace ba.
8- kulawa da damuwarsu da kokarin kawar musu da ita ko nuna musu hanyar da ta dace, kar a barsu su yi kokarin kauda damuwar su da kansu ko ta hanyar abokai.
9- zabar musu da saba musu da lokutan da suka fi dacewa a yi amfani da intanet.
10- hanasu kadaici a mafiya yawan lokatansu tare da daukar matakan da suka dace in aka same su da yin mu'amala da shafukan intanet da basu dace ba.
Abu Ahmad Tijjani Haruna
11/02/2020.
Comments
Post a Comment