Skip to main content

HUKUNCIN GINA TOILET YA FUSKANCI AL-QIBLA

Tambaya

Assalamu alaikum malam mutunne yagina sabon gida saida akagama aikin komai sai yalura ansa toilet yana kallon gabas saiyace acire ajuya amusulunce babu kyau Asa gado ko toilet suna kallon gabas dan Allah malam menene hukuncin haka nagode

Amsa

Wa'alaykumussalam. 
Hadisi ya inganta daga Abu ayubal Ansari a cikin bukhari da muslim cewa manzon Allah ya hana a kallai alqibla ko a bata baya wajen biyan bukata... 

Amma jamhurun malamai cikin su akwai Imam malik, Shafi'i da Ahmad Bin Hambal sunce wannan hanin ya shafi wanda zai biya bukatar sa ne a fili inda babu wani shamaki tsakanin sa da alqibla, amma idan akwai shamaki ko cikin irin bayukan mu toh babu komai...
Sauran Malaman kamar su Imam Abu hanifah sunce hanin ya shafi fili da kuma cikin bayi, wannan shine ra'ayin shehul Islam Ibn Taymiyya, (Aduba Al'Mugny 1\107)..

An tambayi malaman lajna sun bada fatawar babu laifi idan har akwai shamaki wato wani gini ko makamancin sa aduba Fatawa lajna 5\97.
Don haka idan har ka riga ka gina bayin toh babu komai akan ka ba sai ka rusa ba, in kuma kafin ka gina ne to zaka iya gyara tsarin ta yadda zaka kaucewa kallon ka'aba don gujewa duk wata shubuha. 
Amma tunda kace ka gyara shikenan muna fatar Allah ya baka ladar nesantar hanin manzon Allah. 
Zancen saka gado ya kalli gabas ban san wani dalili daya hana haka ba, abinda na sani shine a kwanta a gefen dama kafin ayi bacci a kuma kaucewa kifa ciki. 

Wallahu a'alam.

Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...