Tambaya
Assalamualaikum, tambaya ta, matanane ta haifu lokacin azumi, kamin azumi ya zagayo kuma ta dau Wani ciki bata Samu ta biya Wanda ta sha ba, domin kuwa tana shayarwa kuma ga ciki, ta fara ramawa a wannan halin, ranar farko tana shan Ruwa Sai asibiti dama tana da ulser amma ba Wanda zai Hana azumi ba, ganin haka nikuma Na tsorata Sai Na hanata azumin. Mallam tambaya Na shine 1.inada laifi ne Na hanata azumi 2. Zata Rama azuminne koko shayarwa koko dukka biyu 3. In shayarwa ne zata iya Bawa mutum daya dukkan mudunabi a lokaci daya koko Ko Wani rana za a Bawa mutum daya.
Amsa
Wa'alaykumussalam
1. Ba kada laifi domin shari'a tayi rangwame ga wanda ba yada lafiya da ya aje azumi sai ya rama a wasu lokuttan na daban bayan ya samu sauki, kamar yadda yazo cikin fadar Allah cikin suratul bakara 184.
2. Idan har zata iya ramawa to ta rama duk abinda ta sha, idan kuma bazata iya ramawa ba bisa bincike na likitoci masana addini toh zata ciyar ne kawai babu ramako akan ta, malamai na hujja da fadar Allah suratul bakara 184.
3. Zata ciyar da miskini daya kowane yini, idan kuma ta hada na adadin da ake binta ta baiwa miskini daya duka shima babu laifi, kamar yadda Sheihul islam ibn taymiyya ya bada fatawa cikin littafin sa majmoo'ul fatawa 15/203.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment