Tambaya:
Assalamu alaikum, mene ne matsayin wanda ya yi tafiya umra daga nan Nigeria sai aka daura mai aure alhali yana can Saudia?.
Amsa
Wa'alikum assalam, in har ya zo Saudiyya, amma yana Madina bai dau harama ba, ya halatta a daura masa aure, haka nan idan yana Makka bayan ya kammala umara.
Yana haramta ga mai umara a daura masa aure ne, idan ya tsunduma a cikin harama da umara kafin ya warware, saboda fadin Annabi ﷺ "Wanda ya yi harama kar ya yi aure". Kasancewar shi a Makka ko Madina ba shi zai hana shi aure ba, mutukar bai cakudu da harama ba kamar yadda hadisin ya kayyade.
Allah ne mafi sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment