TAMBAYA:
Assalamu alaikum mallam,Macece takai mijinta kotu akan tanason saki, anyi zama na daya a kotu Sai ya dawo ya saketa agidan iyayen ta, Sai a zama na biyu taje da takardan kotu ta nuna wa alkali, Sai yace mata kotu ta tabbatar da sakin, Sai aka tambayi mijin nata koh akwai wani abun da yake bukata, Sai yace ba komi, bayan kwana biyu Sai yaje ya mayar da ita, ita Kuma tace bazata koma ba, da taje ta samu alkalin ta sanar dashi, Sai yace zabi yana wajenta, toh shi mijin Kuma yana ta ce ma mutane har yanzu akwai auren shi akan ta, tambaya na Shine yaya matsayin auren su a musulunce?
AMSA:
Wa alaikum assalam, to shi dai sakin Alkali babu kome a cikinsa, sai an sake sabon aure, amma tun da anan mijinta ne ya sake ta ba alkali ba, mijin yana da damar da zai mayar da ita, mutukar sakın daya ne ko biyu, kuma bata kammala tsarki na uku ba,
Allah ne mafi sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment