A samu daga Ja'afar al-Saa'ig, ya ce:
Akwai wani mutum makwabcin Imam Ahmad wanda yake mai yawan sabon Allah, sai ga shi wata rana ya zo wajen Imamu Ahmad, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama, ya yi masa sallama, sai Imamu Ahmad bai amsa masa sosai ba, sannan bai mika masa hannu ba.
Sai mutumin ya ce: Yaa Baban Abdullahi, me ya sa baka bani hannu mun gaisa ba? Alhalin na daina aikata abin da kake tsamanina da shi, saboda wani mafarki da na yi.
Sai Imamu Ahmad, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama, ya ce: me ka gani a mafarkin?
Ya ce: Na ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a saman kasa sannan ga mutane masu yawa suna zaune a karkashin shi. Sai wadannan mutanen suna taso daya bayan daya suna zuwa wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, su na cewa ka yi mana addu'a, sai Manzon Allah, Ya yi musu addu'a, har sai da suka kare saura ni kadai.
Ya ce sai na yi nufin in mike ni ma in je in ce ya yi mun addu'a, amma sai na ji kunya ta kama ni saboda irin zunubai da nake aikatawa.
Sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kira ni Ya ce mun: Me ya sa baka taso ka ce in yi maka addu'a ba?
Sai na ce: Babu abin da ya hana ni face kunya na munin abun da nake aikatawa .
Sai ya ce mun: Idan har kunya ce ta hana ka to taso ka zo kai ma ka ce in roka maka Allah DOMIN BAKA ZAGIN KOWA DAYA DAGA CIKIN SAHABBAINA.
Ya ce: sai na mike na je Ya roka mun Allah.
Bayan na farka daga bacci sai na ji ina kyamatar dukkan zunuban da na kasance ina aikatawa.
Sai Imam Ahmad, Allah Ta'ala Ya yi masa rahama ya ce: Yaa Ja'afar, Yaa kai wannan mutum ku bayar da wannan labari kuma ku kiyaye wannan labarin domin zai amfanar.
Ga mai son duba wannan labari zai iya karanta littafin قصص التائبين na babban Malami محمود المصري أبو عمار shafin na 228 ko a duba littafin كتاب التوابين shafi na 178.
Yaa Allah ka tsare mu daga aikata zunubai kuma Ka tsare mu daga ZAGIN SAHABBAN MANZON ALLAH.
Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria.
07/03/2017
Comments
Post a Comment