Skip to main content

YADDA AKE YIN SALLAH A JIRGIN SAMA DA MOTAR HAYA


Tambaya:


Assalamu alaikum Gafarta Mallam ya halatta yin Sallar Farilla a cikin Mota/jirgin Sama da na Ruwa? domin wa su lokutan Mutum ya kan yi tafiya mai nisa zuwa jahohin kudu ga lokacin Sallah ya yi ba sa Tsayawa domin ayi Sallah, sbd ma fi akasarin fasinjojin Ba Musulmai ba ne, kai har direban ma ba Musulmi bane.   


Amsa:


Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta ka yi sallah a jirgi ko mota, idan ya zama ba za ka sauka ba, sai bayan lokacinta ya fita, saboda fadin Allah madaukaki "Kuma Allah ya wajabtawa muminai sallah a cikin lokuta kayyadaddu" Surattunnisa'i aya ta:103. 

Amma mutukar zaka iya riskar lokacinta bayan ka sauka, to ka jinkita ta daga farkon lokacinta, shi ya fi, saboda ka samu damar cika ruku'u da sujjada yadda ya kamata, hakanan idan tana daga cikin sallolin da matafiyi zai iya hada ta da 'yar'uwarta, kamar azahar da la'asar, ko magriba da Isha, saboda za ka iya jinkirta ta farkon, ka yi ta hade da ta karshen.

Duk sallar da ka ji tsoron fitar lokacinta za ka iya yinta a jirgi ko mota gwargwadon yadda ka samu iko, don haka ya halatta ka yi nuni da ruku'u ko sujjada lokacin da kake sallah a mota, idan kuma jirgi ne mutukar ka samu damar yi a tsaye ba za ka zauna ba, sannan ka yi kokari a duka wajan fuskantar alkibla, sai in ya ta'azzara.

Annabi s.a.w. ya halatta yin sallah a jirgin ruwa kamar yadda Albani ya inganta hadisin a Sahihul-jami'i a hadisi mai lamba ta : 3777, wannan sai ya nuna halaccin yi a mota da jirgin sama, saboda dukkansu ababen hawa ne.

Allah ne mafi sani


Amsawa ✍🏻


 DR. JAMILU YUSUF ZAREWA


Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Comments

Popular posts from this blog

Addu'ar Neman Mijin/Matar Aure

TAMBAYA Assalamu Alaikum warahmatullah malam don Allah ina Neman fatawane Watace take Neman miji kasancewar duk masu  zuwa wurinta ba dagaske suke yi ba toh shi ne ta nemi taimako wurin malamin zaure yake bata rubutu tana sha daniyyar Allah ya sa ta dace. Toh malam abin tambaya anan shi ne shin menene makomar abin da ta aikata? shin malam tayi shirka ne ko kuwa tayi ba daidai ba? nagode. AMSA    Dafarko gameda shan rubutu muddin ayan QUR'ANI ne tsantsa babu wasu zane zanen hatimi, to ya halatta yadda IBN TAIMIYYA ya tabbatar a MAJMU'UL FATAWA, haka ma WAHEED ABDUSSALAM BAALY ya tabbar da hakan a SARIMUL BATTAR,    Amma in akasin haka ne haramun ne don yakan zama shirka ne da surkulle,    Fadin cewa Malamin zaure ne na gargajiya to galibi irin na shirkan sukeyi, don haka ki tuba tsakanin ki da ALLAH da alkawarin bazaki sake zuwa wurin su ba don kare addinin ki da mutuncin ki,    Don samun biyan bukatun ki sai kizage da addu'a da kiyamul...

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI Fitowa na 3

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI               NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 3 (kuma fitowa ta karshe): HAKKOKIN MACE A KAN MIJINTA: Kamar yadda miji yake da hakkoki akan matarsa, haka ita ma matar take da hakkokin akan mijinta, daga cikin wadannan hakkoki akwai : 1 - SADAKI: Hakkin mace ne a bata sadakinta, yayin da za a aure ta, Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Ku bawa mata sadakinsu kyauta” (Nisa’i 4). A wani wurin Allah Madaukakin Sarki cewa ya yi:   “Ku aure su da izinin iyalansu, ku basu sadakinsu da adalci” (Addalak : 25). 2 – CIYARWA: Hakkin mata ne akan mijinta ya ciyar da ita, gwargwadon halinsa, koda kuwa tana da wadata da arziki, Allah Madaukakin Sarki yana cewa :  “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuwa aka kuntatawa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya bashi, Allah baya dorawa wata rai sai abin da ya bata” (Dalaq : 7). An tambayi Manzon Allah, tsira da amincin ...

Hakkokin Ma'aurata a Shari'ar Musulunci Fitowa na 2

HAKKOKIN MA’AURATA A SHARI’AR MUSULUNCI       NA MALAM RABI'U UMAR RIJIYAR LEMO, KANO. FITOWA TA 2 3 -  YIN ADO DA KWALLIYA: Hakkin miji ne akan matarsa ta yi masa ado da kwalliya, don ta kare shi daga kallon wasu matan daban, wadanda shari’a ta hana shi kallonsu. Mata sun kasance suna kwalliya da dan kunne da awarwaro da munduwa tun a zamanin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda hadisin Abdullahi dan Abbas, Allah Ya kara yarda a gare shi a cikin Sahihul Bukhari da Muslim ya nuna, a lokacin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya je wajensu, ya yi musu wa’azi a ranar idi. Kuma saboda Mahimmanci mace ta yi wa mijinta kwalliya, ta zama a shiga mai kyau mai jan hankali, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana miji ya dawo wa iyalinsa daga tafiya cikin dare, ya shigo gida ba tare da sun san da zuwansa ba, An karbo daga Jabir, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce, Manz...