Tambaya :
Assalamu alaikum Malam ya halata mahaifina ya aure mace ,ni kuma na auri kanwarta.
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta ka aureta, saboda ba ta cikin mataye guda goma sha biyar wadanda Allah ya haramta a aure su a cikin suratunnisa'ai, ga shi kuma babu wani hadisin da ya haramta a aure ta, Allah yana cewa a cikin suratunnisa'i aya ta: 24, bayan ya ambaci matan da aka haramta a aura, "Duk matan da ba wadannan ba, to an halatta muku ku aure su.
Allah ne mafi sani
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
10\3\2015
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment