Tambaya:
As SALAMUN alaikum, Malamai ya halarta musulmi ya musuluntar da matar da yayi zaman daduro da ita bayan hakan ya aure ta , limanmin da ya goyi bayan hakan yayi daide? Please is very important"
Amsa:
Wa'alaikum Assalamu,
ya halatta sabida babu alaka tsakanin dadironsu da auransu bayan ta musulunta Mutukar sun tuba, saboda musulunci yana rusa abin da ya gabace shi na zunubi kamar yadda ya tabbata a hadisin Amru bn Al'ass.
Idan musulmi ya yi zina ya tuba, to Allah yana gafarta dükkan zunuban da suke hakkinsa ne, kamar yadda aya ta: 53 a suratu Zumar ta tabbatar hakan
Allah ne mafi Sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Comments
Post a Comment