Tambaya:
Salamun alaikum. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?
Amsa:
Wa alaikum assalamu,
To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul.
Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma dakuma yin wanka
Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condom.
Allah ne mafi sani.
Amsawa ✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Comments
Post a Comment